Malamin ya ce yin fim ko waƙa ya halatta kuma jihadi ne sannan akwai ɗumbinlada mai tarin yawa ga wanɗanda ke yin sana ar tasu.
Malamin ya ƙara da cewa matuƙar an gina fim ɗin ko waƙar bisa tsari da koyarwar addinin musulunci to kuwa babu shakka masu yi na kwankwaɗar lada musamman idan suka aike da saƙo mai muhimmanci ga jama a.
Amma akasin hakan kuwa babu abinda zai haifar illa samun zunubi matuƙar ba a gina abin bisa koyarwa ta addinin musulunci ba.
Shek Moriki ya ce ko a zamanin Annabi S.A.W ma an yi waƙe wanda hakan ke nuni da cewa abin ya samo asali.
Amma yin bambaɗanci ko ƙarin gishiri a cikin waƙar haramun ne, inji shek Moriki.
Idan ba ku manta ba kuma a baya bayannnan ma mujallar Matashiya ta tattauna da shugaban hukumar tace fina finai da ɗab’i ta jihar kano Mallam Isma ila Na abba Afakallahu wanda ya ce suna iya bakin ƙoƙarinsu don ganin an tsaftace sana ar tare da karkaɗe bara gurbin ƴan masana antar.
Cikin tsarin da suke kuwa shi ne yin rijinta na kowanme fanni matuƙar mutum zai taka rawa a cikin sana ar hatta ɗan aike.
©HausaLoaded
Post a Comment