Duk A Cikin Shirin 'Yan Fim da Finafinai, Wanda Jaridar Dimokuradiyya Ke Daukar Nauyi

Wakilinmu Mukhtar Yakubu Kano

A satin da ya gabata ne dai aka kammala haska fim din Akeelah wanda Mansurah Isah ta dauki nauyin shiryawa kuma aka haska shi a Sinimar dake cikin katafaren Kantin Shooprite dake Kano, kuma ganin yadda fim din ya samu karbuwa a sinimar ya sa muka ji ta bakin furodusa Mansurah Isah kan yadda haska fim din nata ya kasance.

shin ko kwalliya ta biya kudin sabulu? Sai ta amsa mana da cewar "

To za a iya cewar kwalliya ta biya kudin sabulu, idan aka duba yadda jama'a suka shiga kallon fim din da kuma yadda suka yaba da irin sakon da fim din yake dauke da shi, domin babban buri na shi ne Isar da sakon da fim din ya kunsa.

Amma idan ka duba yadda harkar nuna fim take a Sinima to wani abu ne mai cike da son a sani da kuma iya yi na 'yan fim amma dai ba don a kai Sinima a haska a samu kudi ba.

Mansurah, ta kara da cewa kawai dai ana yi ne don a burge kawaye da abokai amma ba na zaton a yanzu za a kai fim Sinima domin a mayar da kudin da aka kashe domin hanyoyin da za ka bi kafin a karbi fim din naka har zuwa lokacin da za a nuna shi da kuma ma'aikatan da za ka dauka don su kular maka da wajen lokacin haska fim din Ba Karamin caji zaka sha ba, Inji ta.

Ta Cigaba da cewa ana haska fim ne tsawon sati guda kuma a cikin satin kwana uku ne mutane suke cika wajen daga juma'a zuwa lahadi duk sauran kwanakin da za su biyo baya to sai ka ga mutane ba su fi goma ba duk haskawar da za a yi don haka ta ina za a mayar da kudin da aka kashe da har za a yi tunanin cin riba?

Gaskiyar magana idan ma za a samu kudi to sai dai ta bayan fage da wasu za su ba ka a Matsayin gudummawa, amma dai ba ta hanyar nuna fim a Sinima ba.

A baya da ban shiga tsarin ba ban san da haka ba amma yanzu na gane nuna fim a Sinima ba harka ce ta a samu kudi har a ci riba ba sai dai kawai a tallata kai da kuma neman suna".

Dangane da lokacin da fim din zai shiga kasuwa kuwa cewa ta yi" to zai shiga kasuwa nan gaba amma dai ka san yadda lamarin kasuwar yake a yanzu.

Amma dai hakan ba zai karya mini gwiwa ba zan sake shi kuma nan gaba zan ci gaba da fitar da finafinai na fadakarwa domin koyar da mutane darasin rayuwa kamar yadda na yi a cikin fim din Akeelah.

Daga karshe dai Mansura Isah, ta yi godiya ga mutanen da suka bada gudummawa har zuwa lokacin da fim din ya kammala.

©HausaLoaded

Post a Comment

 
Top