Daga Dauda Auwal Isah

Al'ummar Tijjanawa mazauna kasar Amurka, dake birnin New York, sun gina wani katafaren masallaci, da aka kashe miliyoyin dalolin kudade yayin aikin ginin sa.

Masallacin wanda aka yi wa lakabi da sunan babban Sahabin MANZON ALLAH (SAW) wato Sayyadi Abubakar, tuni ya soma jan hankalin al'ummar musulmin duniya, inda tuni musulmi dake fadin birnin New York suka soma hallara cikin sa domin yin ibada.



Al'ummar musulmi Tijjanawa dai sun shahara ne da zaman lafiya a duk inda suka kasance da duk al'ummar da suka kasance cikin ta, wanda hakan ya sanya wadanda ba musulmi ba ma basu shakkun rayuwa dasu.

Idan mai karatu bai manta ba, a makon da ya gabata ne al'ummar musulmi Tijjanawa suka bude wani katafaren masallaci da suka gina a kasar Sengal wanda ke daukar adadin masallata kusan dubu uku, masallacin da babu irin sa a fadin Afrika. Baya ga Gidauniyar ginin cibiyar Addinin Musulunci ta duniya da Sheikh Shariff Ibrahim Saleh ya yi assasa.

Allah Ya daukaka musulunci baki daya. Amiin

©HausaLoaded

Post a Comment

 
Top