A yau bayanin mu akan yadda mace zata mallake mijin ta ne,kuma cikin sauƙi ba kwashe kudi ba kaice hanya ba saɓawa Allah da manzan sa,babu boka babu matsafa.

A zamanin nan da muke ciki yakai ka kawao wasu matan suna so su mallake mazajen su amma sai su afkawa shirka da bata,domin suna komawa bin bokaye yan yan damfara,a karshe kuma su fada cikin nadama 

YADDA ZAKI MALLAKE MIJIN KI.

1.da farko idan kina son mallake mijin ki a matakin farko dole ki zama mai iya kwalliya,domin abinda yake jawo karo aure ko rabuwar aure a wannan lokacin shine akwai rashin yin kwalliya ga mijin ki,wai sai mace tace ai ita yanzu aitayi aure kwalliya kuma sai yan mata, wannan ba daidai bane,ki zama kullum cikin ado ga mijin ki ta yadda ko wata ya gani a waje zaice bata kai matata kyau ba.

2. Ki zama mai tsafta,da yawa wasu matan rashin tsafta ne yake kashe musu aure,zaka ga mace wata idan ta tashi daga barci ko wanka baza tayi ba wai sai yamma,ko kuma kawai ka ganta daga ita sai zani guda daya kullum hakan yana sa mijin ki ya gaji dake har ya fara tunanin kawo wata,amman idan kika zama kullum tsaf tsaf ,kar wai don kina gaban mijin ki ki rika barin jikin ki a bude aa kullum ki zama ciki sutturar ki ta haka ne mijin ki zai fi sha'awar ganin ki a kusa da shi 

3. Biyayya, abu mafi wahala a rayuwar zaman aure shine biyayya saboda da yawa matan yanzu suna da karancin yiwa mazajen su biyayya, a zaman takewar aure ana son macce ta zama tafi mijin ta hakuri koda ya bata miki rai karki nuna baki damu da shi ba,aa ki bashi hakuri a fahimci juna,ta yadda zai san cewa kina son sa kuma kina da biyayya a gare shi idan yace yi to kiyi idan yace bari to ki bari.

4. Iya girki,a wannan zamani namu takai ta kawo wasu matan ma sai an sa musu rana suke fara tunanin tayaya zasu fara koyar girki,kuma wannan kuskure ne,kamata yayi mace ta zama mai taimaka wa mahaifiyar ta a bangaren girki da wasu al'amuran gida ta yadda zata samu damar koyar wasu abubuwa cikin sauki,ta yadda kowanne kalar abincin da mai gida yake bukata zaki iya yi masa shi,abin haushi zaka ga wata ita nada dafa shinkafa da taliya babu abinda zata iya girkawa,wata ma idan ta dafa shinkafar sai ta caɓe,idan kin son mijin ki yaso ki sosai dole ki iya girki ta yadda koda abincin wani guri yaci yaji bai kai naki dadi ba.

5. Soyayya, wasu matan suna dauka idan anyi aure an gama soyaya aa ba'a gama ba karawa zakiyi sai dai duk wadda za'ai baza ai kamar wacce akai a baya ba,amma ki zama mai nuna soyayya ga mijin ki ki rika yi masa yanga da rankwaɗa harda kwarkwasa,ki zama mai yi masa daɗaɗan kalamai masu sanyaya zuciya,bawai ki rika yi masa magana kamar wani kanin ki ba.

Insha Allahu indai kinbi wadannan hanyoyi zaki ga yadda mijin ki zai so ki,kuma koda amarya aka ce ya kawo zaice aa tawa ma da ishe ni.

Allah yasa mu dace Allah ya bami ikon yin biyayya a gare shi.

Allah ya barmu da Annabi Muhammad Sallallahu Alaihi wasallam.


Sirrin Rike Miji islamic medical center 
☏+2348037538596



© Sirrinrikemiji

Post a Comment

 
Top