Legit ta ruwaito,Wani sabon lamari ne a kasar Turawa ace budurwa wacce ta tashi cikin addinin Kiristanci ta auri Musulmi. Ba kuma a nan lamarin ya tsaya ba, domin kuwa ita ma ta koma addinin Musuluncin, kuma ta Musuluntar da dukkanin danginta, haka kuma ta Musuluntar da akalla abokananta da makwabta guda talatin

Matar mai suna Aisha Bhutta, wacce aka fi sani da Debbie Roger, ita da danginta cikakkun masu bin addinin Kiristanci ne, a yayin da kowa ya shagala da addinin Kiristanci, ita kuma Aisha a lokacin taji hankalinta ya kasa kwanciya, inda ta dinga tambayar kanta abubuwa da yawa wadanda ba ta da amsar su. "Gaskiya akwai abubuwan da ya kamata na fuskanta, ba kawai na dinga yin ibada ba a duk lokacin dana ga dama."

Aisha ta hadu da mijinta Mohammed Bhutta, a lokacin da take 'yar shekara 10 kuma take yawan zuwa shagon shi. Tana yawan ganin shi yana sallah idan taje. "Akwai nutsuwa da wani boyayyen abu a sallar da yake yi. Ya ce mini shi Musulmi ne, na tambaye shi menene Musulunci?"


A hankali a hankali da taimakon Mohammed, Aisha ta yi zurfi a cikin addinin Musulunci. A lokacin da ta kai shekara 17 a duniya ta haddace Al-Qur'ani mai girma baki daya. "Duk abinda na karanta yana bayar da ma'ana," in ji ta. Ta dawo addinin Musulunci a lokacin da take da shekara 16 a duniya.

"Duk lokacin dana karanta sai naji tamkar an sauke mini wani nauyi ne a kai na, sai naji na dawo tamkar jaririya sabuwa."

Sai dai kuma duk da ta Musulunta, iyayen Mohammed sun ki yarda ya aureta, saboda suna yi mata kallon baturiya za ta iya lalata musu yaro. Amma duk da haka sunyi auren, inda aka daura auren a wani masallaci.



"Ni da mijina ne muka yi iya yin mu wajen ganin iyaye na sun dawo addinin Musulunci, cikin kankanin lokaci mahaifiyata ta Musulunta, inda ta canja sunanta zuwa Sumayya."

"Ni da mahaifiyata haka muka cigaba da jawo ra'ayin mahaifina. Wata rana muna zaune muna hira kawai sai ji muka yi yace 'Wacce kalma ce ake furtawa idan za a shiga addinin Musulunci?"


"Dan tsananin murna bamu san lokacin da muka yi tsalle muka haye kan shi ba."

Bayan shekara uku, Yayan Aisha shima ya Musulunta sannan ya Musuluntar da matarshi da 'ya'yanshi, sannan dan gidan Yayarta shi ma ya Musulunta.

Bayan ta gama Musuluntar da danginta gaba daya, sai ta koma kan Makwabta da Abokananta, inda ta shafe kusan shekara 13 tana koyar da addinin Musulunci, zuwa yanzu dai Aisha ta Musuluntar da Abokananta akalla guda 30.

Wani babban malamin jami'ar Glasgow mai suna Trudy, yana halartar koyarwar da Aisha take yi saboda wani bincike da yake yi akan addnin Musulunci, amma kuma cikin ikon Allah kawai sai gashi shima ya Musulunta.

©HausaLoaded

Post a Comment

 
Top