Soyayyar da take tsakanin Darakta Kamal S Alkali da jaruma Hauwa S Garba ba boyayyiya ba ce a cikin masana'antar Kannywood kasancewar kowa ya san yadda suka shafe tsawon lokaci suka soyayyar su, kuma duk wanda ya ke a cikin masana'antar ya san irin alakar soyayyar da ake yi tsakanin masoyan biyu don kuwa matsayin soyayyar ta su ya kai ta yadda duk in da ka ga Hauwa S Garba, to kana dubawa gefen ta za ka ga Kamal S Alkali. Idan kuwa labarin daya kake bukata, da zarar ka ga daya daga cikinsu ya wadatar.

To amma abin da ya fi daure wa mutane kai dangane da soyayyar Hauwa S Garba da Kamal S Alkali shi ne soyayya ce ta yaudara ko kuma ta aure ce? Domin kuwa idan ta aure ce a yadda suka shafe zama da shekara biyar suna soyayya to ya kamata a gani a kasa, game da maganar aure, in kuma ta yaudara ce to cikin su wa yake yaudarar wani? Ko dai suna yaudarar juna ne.

A bangaren Kamal S Alkali dai kowa ya san Darakta ne da a baya ya yi soyayya da irin su Fati Washa, wanda ta dalilinsa ta samu karbuwa sosai a tsakanin ‘yan fim da jama’ar gari.​

Sai dai ta bangaren jaruma Hausa S Garba, har yanzu ba ta samu dama irin wadda Fati Washa ta samu ba, domin Kamal S Alkali bai ba ta damar ta yi suna a harkar fim ba sai dai kawai sunan da ta yi a cikin masana'antar, shi ya sa wasu ke ganin ko dai daraktan jarumar suna kokarin shigewa daga ciki ne.

Majiyarmu ta rawaito cewa ita ma Hauwa ba da shi kadai take soyayya ba, amma dai tana yi ne ta bayan gida ba tare da ya sani ba, duk da yake wani lokacin ba zai rasa sani ba sai dai ya kawar da kai don gudun bacin ranta.

Ko da muka tambayi Hauwa S Garba kan matsayin soyayyar su da Kamal S Alkali da kuma baton yaudarar juna da ake kallon suna yi sai ta ce, “Babu wani yaudarar juna da muke yi, mutane ne dai kawai suka saka mana ido, kuma sai dai kawai su gan mu tare don ba za su iya raba mu ba, kuma aure nufin Allah ne. Duk lokacin da Allah ya kawo za a yi, don haka mutane su daina yi mana wata doguwar fassara.”

Shi ma Kamal S Alkali da muka tambaye shi kan maganar soyayyar su da Hauwa S Garba, cewa ya yi, “Mutane su zuba ido nan gaba kadan za su ga abin da zai wakana don haka su daina gaggawa ko fadar magana da ba ta da tushe da asali.”

©HausaLoaded

Post a Comment

 
Top