A safiyar yau Talata 1 ga watan Oktoba 2019, wanda ya kasance Najeriya tana da shekaru 59 da “samun Yanci”Shugaba Muhammadu Buhari ya yi kira ga  yan Najeriya da su hada hannuwansu tare da marawa gwamnati baya domin samun cigaban kasar ta Najeriya a nan gaba.
Shugaban Buhari yayi  murnar cikar Najeriya shekaru 59 da samun ‘yancin kai,  inda yace, Najeriya za ta farfado daga cikin halin da ta jima cikinsa na tsanani nan bada jimawa ba. Sannan  yayi kira ga yan Najeriya su kara hakuri sannan  kuma suyi amfani da hanyoyin da ya  dace wajen  isarwa  gwamnati duk  korafe-korafensu da suke dashi.

Buhari ya kara da cewa, dukkan wani  hankalinmu yanzu a kan masu aikata muggan laifuka ta hanyoyin zamani wato yanar gizo, sannan  kuma masu yada labarai marasa tushe a shafukan sadarwa na zamani. Duk da cewa muna cigaba da mutunta kundin tsarin kasarmu wanda ya halarta ‘yancin fadin albarkacin baki ga ko wane dan kasa, amma kuma ba za mu zuba muna kallon wadansu tsirarun mutane na neman haddasa fitina a kasar ba.

Shugaba Buhari ya kara da cewa: Kiyayya da ganin kyashi ba komi take haifarwa ba in banda tabarbarewar kasa da kuma rashin cigaba. Ina da yakinin cewa akasarin yan Najeriya sun fi sha’awar zaman lumana da kwanciyar hankali a junasu.
A jawabin da ya gabatar ga 'ya kasar ta talabijin din Najeriya da misalin karfe 7:00 na safe, shugaban mai shekara 76, ya ce gwamnatinsa ta sha alwashin kare hakkin kowanne dan kasar.

A karshe yace, kaddamar da kasafin kudin 2019 wanda aka yi a watan Yuni zai soma aiki cikin gaggawa domin ganin cewa an kammala ayyukan manya masu matukar amfani ga al’ummar  kasar ta Najeriya baki daya.

©HausaLoaded

Post a Comment

 
Top