Northflix ta ruwaito.A daidai lokacin da ake cikin wani yanayi a cikin masana'antar finafinai ta Kannywood, kwamitin Dattawan Kannywood a karkashin jagorancin Malam Auwala Mashal sun fara zama domin ceto masana'antar daga halin da ta samu kanta a ciki domin daidaita alkiblar ta.

A karshen makon nan dai Dattawan suka zauna a wajen taro na Hazain daga cibiyar gidan gona a Kano, inda suka shafe tsawon lokaci suna yin bitar matsalolin da suka dabaibaye harkar ta bangarori da dama, wanda hakan ya mayar da masana'antar ta shiga cikin wani hali na rashin tabbas.

Kusan shekarun masu yawa kenan ana ta kokarin ganin an masana’antar Kannywood na gamuwa da kalubale kala-kala; kasuwanci, rikicin gida da kuma sabanin tsakanin masu sana’ar da gwamnatoci.

Da yake yi wa wakilin mu bayani dangane da zaman na su, Shugaban kwamitin Dattawan, Malam Auwalu Mashal ya ce manufar zaman nasu shi ne zayyano kalubalen masana’antar tare bitar su daki-daki don ganin a magancen su.

Ya ce: “A yanzu mun samu kanmu a cikin wani yanayi a cikin masana'antar finafinai ta Kannywood wanda ba a san inda ta sa gaba ba, domin yanzu ana cikin yanayi na rigima tsakanin ‘yan fim a junan su ga kuma rigimar da ta kunno kai a tsakanin wasu mambobin kungiyar da Hukumar tace finafinai ta jihar Kano sakamakon tsarin yin rajisata da ta bullo da shi.

“Wadannan da ma wasu matsaloli da suke tasowa muka tsara yin wannan zaman a matsayin mu na Dattawan harkar, kuma a yanzu ba mu kai ga cimma matsaya ba amma dai za mu ci gaba da zama irin wannan domin samar wa da masana'antar alkibla, don haka muna fatan za mu samu hadin kai daga dukkanin wanda harkar ta dame shi.”

Taron dai ya samu halartar manyan Dattawan harkar da suka hada da Mai Unguwa Alhaji Ibrahim Mandawai, Dan'azumi Baba, Malam Habibu Sani, Kabiru Maikaba da sauran su.

©HausaLoaded

Post a Comment

 
Top