Duk da kasancewar Adam Zango bai taya Ali Nuhu murnar zagayowar ranar haihuwarsa ba a watan Maris din da ta gabata, sakamakon rashin jituwar da ke tsakaninsu, Alin ya yi dattaku, inda ya sanya hoton Adamun a shafinsa na Instagram tare da taya shi murnar zagoyawar ranar haihuwarsa a jiya Tamara, 1 ga watan Oktoba.
Adamun ya amsa karamcin da Alin ya yi masa cikin girmamawa, inda ya kira Alin da "Sir"
©HausaLoaded
Post a Comment