DAGA Bashir Abdullahi El-bash

Yau Asabar, 5 ga watan Satumba, 2019.
Tsohuwar mai ba gwamnan Jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje shawara kan harkokin kyautata rayuwa da walwalar mata, kana babbar jaruma, kuma jigo a masana'antar shirya fina-finan Hausa ta (Kannywood), Hajiya Rashida Adamu Abdullahi wacce aka fi sani da (Mai Sa'a), ta yi bayanai kan gamsuwarta da kyawawan halaye da ɗabi'un mai girma gwamna da kuma salon tafiyar da gwamnatinsa.

Daga cikin bayanan da ta yi, Rashida Mai Sa'a ta bayyana cewa kaf faɗin Jihar Kano da ma ƙasa gaba ɗaya ba ta da wani uba kuma jagora sannan fitilarta a siyasa da ya wuci mai girma gwamnan Jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje.

Rashida (Mai Sa'a), ta bayyana dalilanta da cewa, "mai girma gwamnan Jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, shugaba ne nagari mai matuƙar ƙanƙan da kai, (ba shi da girman kai). Kuma shugaba ne da ya ke matuƙar girmama manyan mutane a Jihar Kano da ma ƙasa gaba ɗaya. Sannan kuma shugaba ne da ya ke matuƙar mutunta ƴan adam komai kashinsu, (ba ya raina mutane)".

Sai kuma ta cigaba da cewa, "Gwamna Ganduje, shugaba ne da ya ke matuƙar girmama malaman addinin musulunci da kuma ba su kima da daraja matuƙa a matsayinsu na masana magada Annabawa. Kuma shugaba ne mai matuƙar ƴin hidima da ɗawainiya wajen ciyar da addinin Musulunci gaba, shi ya sa ma ake yi masa laƙabi da (Khadimul Islama).

A fannin ayyukan raya Jiha kuwa, mai Sa'a ta bayyana cewa: "Gwamna Ganduje, shugaba ne nagari wanda ya damu da rayuwar al'ummarsa, duk ayyukansa babu farfaganda irin ta gwamnatin baya, aiki kawai ya ke yi gadan-gadan tsakanin shi da Allah da duba makomar ƴaƴa da jikoki, ko kaɗan babu ƙarya ko zulaƙe cikin ɗumbin ayyukan alkhairan da mai girma gwamna Ganduje ya ke shimfiɗawa a Jihar Kano, kuma al'umma sun shaida".

Da ta ke tsokaci game da cigaban rayuwar mata kuwa, Mai Sa'a ta shaida cewa: "Gwamnatoci da dama sun bar mata a baya cikin damawa da su da kuma kyautata nasu rayuwar, amma mu a Jihar Kano, Babanmu Gwmna Ganduje ya ba mu gata da dukkan wata kulawa da za ta taimaka wajen ciyar da mu gaba".

Idan aka yi duba da dukkan wasu tsare-tsaren mai girma gwamna na tallafawa al'umma su samu ilimi da sana'a, za mu ga akwai mata a cikin duk wani shiri da mai girma gwamna ya ke aiwatarwa. Sannan kuma ga muƙaman gwamnati duk gwamna Ganduje ya ba wa mata dama ana damawa da mu a sassan ma'aikatu da hukumomin gwamnati daban-daban".

"Haka zalika Gwamna Ganduje ya samar da tsare-tsare masu kyau a fannin lafiya domin kulawa da lafiyar mata da jarirai da yara ƙanana, sannan babu wani fannin gwamnati da mai girma gwamna bai yi la'akari da mata ba domin kyautata rayuwarsu. Idan jama'a za su iya tunawa, ko da a baya-bayan nan ai mai girma gwamnan Jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya bayyana ƙudurinsa na ginawa mata Kwalejin koyon ayyukan fasaha da ƙirƙire-ƙirƙire tasu ta kansu (mata zallah) domin su ma ka da a bar su a baya cikin tafiya da sana'o'in zamani".

Dan haka gwamna Gwanduje uba ne, kuma shugaba ne, sannan kuma shi ne jagora, kana kuma fitilarmu a siyasa, mu na ƙaunarsa fiye da yadda ya ke ƙaunarmu, mu na kuma alfahari da shi.

Inji Hajiya Rashida Adamu Abdullahi, wacce aka fi sani da (Rashida Mai Sa'a) tsohuwar mai ba gwamna shawara kan harkokin kyautata rayuwa da walwalar mata a Jihar Kano.

©HausaLoaded

Post a Comment

 
Top