ALLAH ya yi wa mahaifin fitacciyar jaruma Maimuna Mohammed (Watayarinya) rasuwa a ranar juma'a

Jarumar ta tabbatar wa da mujallar Fim cewa mahaifin nata, Alhaji Muhammad Hameed, ya rasu ne a yau a Kano bayan sallar Azahar.

Shekarun sa 60 a duniya.

An yi masa jana'iza a unguwar su Maimuna ɗin, wato Tishama.

Maimuna ta ce Alhaji ya yi fama da rashin lafiya, inda ta yi jinyar sa na wani lokaci.

Allah ya jiƙan sa, amin.

©HausaLoaded

Post a Comment

 
Top