Rahoton jaridar Dabo FM ta bayyana cewa Malaman na Izala sun ziyarci Sambo Dasuki ne a gidansa dake babban birnin tarayya Abuja kwanaki uku da sakinsa da gwamnatin tarayya ta yi bayan kwashe fiye da shekaru hudu a hannu yana tsare kan zarginsa da hannu cikin badakalar kudin makamai.
Gwamnati na zargin Dasuki da laifin mallakar miyagun makamai ba tare da ka’ida ba, tare da hannu cikin badakalar kudi naira biliyan 35 da kuma satar kudi dala biliyan 2.1 da aka ware domin sayen makamai don yakar Boko Haram.
Majiyar Legit.ng ta ruwaito shugaban Izala, Bala Lau, ya bayyana Dasuki a matsayin guda daga cikin mutanen da suka taimaka ma kungiyar wajen ayyukanta na da’awa tare da yada addinin Musulunci a lunguna da sakon kasar nan, don haka yace duk aikin alherin da kungiyar ta yi, Dasuki na da kamashon lada.
“Sai Allah Ya bawa Sambo kamasho saboda duk ayyukanka ne wannan, muna ta yada addinin Musulunci da yin wa’azi, Allah madaukakin Sarki Ya baka lada, Ya kuma kara ma da hakuri. AllahYa bada hakuri, Allah Ya bada hakuri. Mun shigo gari, shi yasa muka zo a kungiyance mu nuna maka lallai abin da aka yi mana ba zamu manta ba.” Inji shi.
Daga cikin wadanda suka kai ziyarar jajantawar ga Sambo Dasuki akwai: Sakataren kungiya, Sheikh Muhammad Kabiru Gombe, Sheikh Yakubu Musa da sauran jiga jigan kungiyar.
A wani labarin kuma, jim kadan bayan fitowarsa daga hannun hukumar DSS, mashawarcin tsohon shugaban kasa Jonathan a kan harkar tsaro, Kanal Sambo Dasuki ya bayyana cewa a shirye yake ya fara kare kansa a gaban kotu.
©HausaLoaded
Post a Comment