Ta yi gargaɗin cewa idan har ba a ɗauki babban mataki ba, to babu yadda za a yi a samu ci-gaba a harkar.
Rahama ta yi wannan kalami ne a wata hirar musamman da ta yi da mujallar Fim.
Jarumar, wadda kuma ita ce furodusar fim ɗin 'Rariya', ta ce, "Gaskiya babu maganar ci-gaba a masana’antar fim a wannan lokacin da mu ke ciki. Saboda idan ka duba gaba ɗaya idan furodusa ya yi fim a wuri ɗaya ya ke iya saida fim ɗin sa - siniman Kano.
"Mu na da jihohi 19 a Arewa, kuma duk su na kallon fim. A wani lissafi da aka yi, an fi kallon finafinan Hausa a kan na Kudu. Amma wannan kasuwar ta lalace, sinimar kawai ake iya kallon fim.
"Shin fim ɗin da ka yi ɗan Kano kawai ka yi ma wa? Ina sauran jihohin da su ma su na da buƙatar kallo?
"Idan ba ku manta ba, na yi ‘Rariya Tour'; in ka ga mutanen da su ka zo su ka kalla... mun je Yola, mun je Gombe duk mun nuna, amma saboda rashin gidajen kallon ba a kai masu finafinai.
"Yanzu sai dai ka yi fim kawai ɗan Kano ya kalla. Don haka ka gaya mani ta inda ci-gaba ya ke. Wanda a da kai ka san idan ka yi fim ka buga sidi da fim ɗaya sai ka yi kuɗi.
"Ban da yanzu, saboda kowa ja baya ya ke yi, babu wanda zai zuba kuɗin sa ya yi fim, kuɗin su ƙi fitowa."
Da mujallar Fim ta tambaye ta shawarar da za ta bayar don a shawo kan wannan matsala, sai Rahama ta amsa da cewa ko dai a koma amfani da hanyar intanet wajen tallata finafinan ko kuma a gina gidajen sinima aƙalla guda biyar a Arewa, maimakon guda ɗaya rak da ake amfani da ita a Kano.
Ta ce: "Kullum in mu ka zauna mu na magana, na kan ce dole sai mun haƙura mun tafi 'digital', kamar yadda duniya ta tafi.
"Idan ba za a yi 'providing' sinimu da yawa ba, a yi ko da guda biyar ne a garuruwan da aka san cewa sun fi kallon finafinan Hausa.
"Idan kuma ba za a yi wannan ba, sai dai mu tafi 'digital'. Saboda duk furodusan da na haɗu da shi, sai na tambaye shi, 'Ka na da dibidi a gidan ka?' Bai da shi! Kowa a waya ya ke kallo. Sai a nemi hanyar da za a tafi 'digital' ɗin da ɗan kallo zai sa a wayar shi ya kalla. Wannan shi ne kaɗai mafita."
Ta ƙara da cewa, "In kuma ba za a iya wannan ba, gwamnati ta yi haƙuri, ta daure - saboda mu na biyan haraji, babu kamfanin da zai yi fim bai biya haraji ba; duk da ban dai sani ba, amma ni ina biya - a daure a gina mana sinimu ko da guda biyar ne a gani, a ce yau wancan ya saida dubu biyar a Kano, ana yi maka maganar miliyoyi ne.
"Wannan shi ne mafita, in ba shi ba sai dai a haƙura."
©HausaLoaded
Post a Comment