Kasancewar an shigo lokacin sanyi a wasu bangarori hakan yana haifar da yamutsewar fata. 

Yana da kyau idan aka yi alwala sai a sake shafa mai domin rage gautsin fata da yamutsewarta. Sakamakon haka ne ya sanya na kawo muku hanyoyin da za a bi don magance yamutsewar fata kamar haka:


• Man ‘moisturizer.’ yana da kyau a samu irin wannan man domin yana taimakawa wajen gyara fata.

• Ruwan fandesho; yana da kyau a rage amfani da fandeshon saboda yana feso kuraje a fuska. Ya kasance an shafa kayan ado kadan a fuska.

• ‘Cleanser;’ idan za a yi amfani da ruwan goge fuska a samu wadanda sinadaransu ba su da karfi domin yin haka yana sa yamutsewar fuska.

• Yana da kyau ya kasance ana amfani da sabulu wanda sinadaransa ba su da karfi. Kamar amfani da sabulan jarirai wajen wanke fuska.

• A wannan lokaci fata na yawan yin duhu yana da kyau ya kasance ana yin dilke da kurkum domin taimakawa wajen haskaka fata a gargajiyance.

• Man kadanya; za a iya amfani da man kadanya a fata. A hada shi da man zaitun sannan a rika shafawa. Ko a narka sai a zuba a man shafawa domin rage warinsa.

• Glycerin; domin kaushin kafa za a iya gauraya shi da man basilin sannan a wanke kafa da dutsen goge kafa da ruwan dumi. Bayan haka sai a shafa a tafin kafa sannan a saka safa. Haka za a rika yi domin rage kaushin kafa.


© Sirrinrikemiji

Post a Comment

 
Top