Ta ce kowa da ra'ayin sa, kuma ko me ta yi sai wani ya yi ƙorafin cewa ba ta yi daidai ba, shi ya sa ta ke yin abin ta gaba-gaɗi.
Shahararriyar jarumar kuma furodusa a masana'antun finafinai na Kannywood da Nollywood ta bayyana haka ne a wata hirar musamman da ta yi da mujallar Fim.
Rahama Sadau dai ta na ɗaya daga cikin ‘yan fim ɗin da duk abin da su ka yi ya kan zama abin surutu a gari, musamman a kafafen sadarwa na zamani.
Ko kwanan nan da ta ɗora wasu hotunan ta a Instagram da Facebook, lokacin da ta ƙaddamar da wani gida mai ɗauke da kamfanonin ta mai suna 'Sadauz Home', sai da aka dinga ce-ce-ku-ce a kai. Mutane da dama sun ce shigar da ta yi ba ta dace ba.
Da mujallar Fim ta yi mata tambaya kan irin wannan yamaɗiɗin da ake yi a kan ta, sai Rahama ta ce, "Wallahi mutane ke jin surutun, ba ni ba.
"Kamar yadda ka ke magana, haka jiya wani ya zo ya na tambaya na, har ya ke cewa in faɗa masa inda na ke samun 'courage' da har ya ke gani na ina dariya.
"Ni ba na gani, mutane su ke gani! In mutum miliyan za su yi magana, wallahi ba na gani. Saboda da na ɗora abu na ke yin gaba.
"Saboda yadda na riga na ɗora wa kai na, duk abin da ka yi wallahi sai an yi magana a kai. Yau idan hijabi na saka a jiki na, wallahi sai an yi magana a kai. So, kawai 'just be yourself', shi ne."
Kyakkyawar jarumar kuma 'yar kasuwa ta yi nuni da cewa duk surutun da za a yi a kan mutum a soshiyal midiya ai ba ya ma daɗewa. Ta ce, "Magana ne da ba daɗewa za a yi ba an daina yin shi an ɗauki wani kuma an ɗora a kai."
Ta ce abin baƙin ciki ne a yau yadda mutane su ke bada muhimmanci kan maganar wani can daban wadda ba ta shafe su ba.
Ta ce: "Ba wani abu da yanzu mutane su ka ɗauke shi da muhimmanci sama da magana: wannan ya yi magana, wancan ya yi magana. Ni ba na ma ɗaukar shi wani abu; da na yi na wuce."
A game da irin kiran da za ta yi ga masu irin wannan halayyar ta damuwa da abin da bai shafe su ba kuwa, sai ta ce, "'Opinion' ne, 'opinion' ni na ɗauke shi. Kuma soshiyal midiyan da ka ke magana, 'Instagram standard' ne, a wurin ne kawai za su yi magana. Babu wanda zai zo ya tare ka 'face-to-face' ya yi maka magana, bai isa ba wallahi! Iyakar sa fa Instagram, to me zai dame ka?
"Kawai dai abin da na ke so a gane, shi fa mutum kowa da rayuwar sa, kowa da 'choice' ɗin sa, kowa da irin abin da ya ke so a rayuwa. Ni ba zan iya sa maka ra’ayin son kaza ba, kai ma ba za ka iya sa mani ra’ayin son kaza ba. Don haka in ka yi magana a kai na, ra’ayin ka ne ka ji ka na so ka yi, in ka zage ni ra’ayin ka ne.
"Don haka na ce kowa ya na da 'opinion', kuma 'everybody’s opinion should be respected'.
"Amma irin waɗannan abubuwan da ke faruwa, gani na ke akwai 'issues' da dama da su ka fi wannan. A wuri na, ɓata lokaci ne ka tsaya ka na maganar wani."
©HausaLoaded
Post a Comment