Shafin Legit ya kawo rahoto Jarumi Isa A. Isa yayi wata babbar magana a wani sabon bidiyo da ya wallafa

- Inda ya bayyanawa mutane masu yawan tambayarsa dangantakar dake tsakaninsa da Sadiya Haruna

- Jarumin ya bayyana cewa daga yau kowa ya sani cewa Sadiya Haruna matarsa ce

Wani bidiyo da jarumin fina-finan Hausa na masana’antar Kannywood yayi ya bayyana dangantakar dake tsakaninsa da Sadiya Haruna, buurwar da ta ware waken bayar da shawarwari akan zaman aure da yadda mace zata rike miji ba tare da samun matsala ba.

Jarumin dai ya bayyana cewa ana yawan tambayarshi dangantakar dake tsakanin shi da Sadiya Haruna, to yaş shine yayi alkawarin bayyanawa, ga abinde jarumin ya ce:

Assalamu Alaikum Warahamatullahi Ta’ala Wabarakatuhum, jama’a kowa ya taso sai ya fara tambayata Isa wai yaya dangantakarshi tsakanin shi da Sadiya, kowa ba shi da aiki sai wannan, saboda haka daga yau ita matata, nagode.”


Ana yawan ganin jarumin da Sadiya Haruna suna yawo tare ko kuma suna daukar hoto ko bidiyo tare.

Idan ba a manta ba Sadiya Haruna dai ita ce wacce jami’an ‘yan sanda suda kama ta kwanakin baya, bayan zargin ta da aka yi da yiwa casu manyan jaruman Kannywood kazafi akan abin basu ji ba basu kuma gani ba.

To amma kuma abinde jarumin ya fada ya bar wası mutane da yawl a cikin duhu, domin kuwa babu wanda yasan lokacin da suda yi aure, ko kuma wani wanda ya halarci daurin auren su, hakan ne ma ya sanya wasu mutane ke kalubalantar shi akan ya bayyana yadda aka yi ta zama matarsa.

©HausaLoaded

Post a Comment

 
Top