Gyaran jiki musamman ga mace na da muhimmanci sosai. 

Domin mata da dama wadanda suke da kananan shekaru idan jikinsu ba ya samun sinadaran da suka kamata akwai matsala. 

Sai a ga fatar jiki tana yankwanewa. 

Yankwanewar fatar na sanya mace tsufa da wuri.

 Don haka, dole ne a rika kula da fatar jiki da gashi da sauran gabobi.

• Gashi; a samu ayaba da kwai a cire kwaiduwar sannan a kwaba tare da ayaba sai a tsaga gashi a shafa a fatar kai hade da gashin kai sosai. A bari na tsawon minti goma zuwa ashirin sannan a wanke da man wanke gashi. Yin haka na sanya karfin gashi kuma yana hana shi zubewa sannan yana sanya shi sheki.

• Farce; a samu zuma a rika shafawa a farce na tsawon minti biyar akalla sau daya a mako domin sanya farce laushi da sheki sannan za a iya shafa zumar a fuskar domin magance kurajen fuska.

• Dilke; a samu dilke a rika shafawa a jiki kamar sau daya a mako, yin haka zai sanya fata santsi da sheki.

• Tsayin gashi; a samu man kwakwa a rika yin kitso da shi ko a rika shafawa a fatar gashi duk lokacin da man ya shanye a kai. Yin hakan na sanya laushi da kuma tsawon gashi.

• Kurajen fuska; a samu lemun tsami a yanka shi gida biyu sai a diga zuma kamar digo daya zuwa biyu. 

Sannan a shafa a kan fuskar na tsawon minti biyar. Sannan a wanke. Za a iya yin wannan da dare kafin a kwanta barci a kullum.

• Fata; yawan shan ruwa na wanke maikon jiki sannan yana sanya fata lafiya. A kasance ana samun isashen barci a kullum domin samun fuska mai sheki.

• Domin kodewar fata; a samu lemun zaki a rika shafawa a inda matsalar take kamar sau biyu a kullum har sai wajen ya kode.


© Sirrinrikemiji

Post a Comment

 
Top