.
Ni a da in aka ce yarinya ta yi aure ba ta iya girki ba sai na zaci diyar masu kudi ce, domin akan dauki ma'aikata da za su kula da komai na cikin gida saboda wadata, yarinya sai dai a kawo mata ta ci, in ta gama a zo a kwashe kwanonin.
.
Amma 'yan matsalolin da ake fama da su a 'yan kwanakinnan na fara dawowa daga fahimtata ta baya, don mun sami wasu sake-sake da aka yi ta samu a sanadiyyar rashin iya girkin da amaren ke fama da shi, na yi hira da wasu magidanta da suka tabbatar min da cewa har alhini suke yi idan wani cikin abokansu ya nuna yana sha'awar ziyartarsu, ba don komai ba sai irin nau'in abincin da za su fito wa baqin da shi.
.
Wani kuwa cewa ya yi: Babban abinda matarsa ta fi iyawa shi ne Indomie, kuma abinda ake dafa wa baqi kenan, domin duk wani canji da za a samu zai iya kawo matsalar da ba a zata ba.
.
Yaran masu kudi dai wai suna da ma'aikata, sai yarinya ta yi kwanciyarta tsawon rayuwarta, sai ta zo aure sai a kai ta wurin koyon zaman gida ta yi 'yan makwanni shikenan ta gama gwanancewa a fahimtarsu, ka ji daure wa qarya gindi.
.
Wata qanwata gwana ce a irin wadannan dafe-dafen, ita take ce min wai an kawo wata 'yar masu hali ta yi rijista, a qarshe ta ce ba ta jin dadi, kashe gari da ta tashi zuwa sai ga ta da 'yar aikinta da za ta yi mata wanke-wanke da 'yan yanke-yanke.
.
Ba na gardamar cewa za a iya koya wa mace girki da irin kayan zaqaqa abinci ko qansata shi wadanda muke da su a yau, matuqar dai za a kawo su to za ta iya hadawa, ko ni nakan dafa irin wancan indomien don akwai komai zubawa kawai zan yi.
.
Amma ya za a yi abincin ya yi dadi a lokacin da babu irin wadannan kayan hade-haden, ko in maigida ba ya son su, ko ba zai juri siyansu ba, ko sun sami kansu a inda ba wanda zai kawo nau'ukan kayayyakin da ta saba da su?
.
Duk mu ajiye wannan a gefe guda, mu manta da karayar arziqi da take samun mutum a wasu lokuta, mu tambayi kammu: "Wai in an koya mata iya hada magi a abinci yadda zai yi dadi a cikin dan qanqanin lokaci, ya za a yi a cire mata qyuya kuma cikin shekara daya? Da kamar wuya.
.
Duk wata tsohuwar hannu ta san me nake cewa, gyaran daki da ban-daki, shirya gida da mai-gida, gyaran kai da kaye-kaye ba abu ne na dan qanqanin lokaci ba, yadda ake karatun boko tun yaranta hake ake yin na zaman gida har digirgir ba ma digiri ba.
.
In mace ba ta yi karatun yaranta ba ta tsallake ta sara a sama kamar wanda zai yi sakandare ne bai yi furamare ba, dole tasirin zai riqa bayyana daga lokaci zuwa lokaci, shi ya sa muke ganin in ba ki koya wa diyarki ba kin cuce ta.
.
Sai ki qure karatun bokonki wace ba ta taba shiga aji ba ta yi miki lakca a kan: Namiji, miji, uwar miji, 'yan uwansa, girki, tsafta, tarairaya, yauqi da kisisina, wani sa'in ba ki da mafita sai kin bi koyarwar da take ba ki sau da qafa.
.
Mata ku koya wa yaranku: Tsafta da tsaftacewa, wanki da wanke-wanke, gyara da gyare-gyare, qamsatuwa da qamsatarwa, ba abinda yaranmu suka gwanance kamar kwalliya, amma shin irin wace maigidan yake so ake masa? 
.
Don Allah kar ki cutar da diyarki, duk halin da kuke da shi yaranku mata su shiga cikin ma'aikata, komai na gida da su za a yi tun yaranta har sai sun yi aure, in ta so su canja amma a can, gidan uwarta makaranta ne da za ta koyo zamantakewa.


By
*MIFTAHUL ILMI*




© Sirrinrikemiji

Post a Comment

 
Top