Gajeriyar tattaunawar Northlix da Darakta Alee Gumzak

Ya kake kallon masana'antar fim a halin yanzu?

Kannywood a halin yanzu kokari ake yi a saita ta yadda ya kamata, saboda mutane sun gano a hadu wuri guda domin kawo karshen matsalar ta hanyar yin rajista da Hukumar Tace Finafinai ta Kano, domin kowa ya samu lasisi na cewar shi din dan cikin masana'antar ne, don rage samun kananan maganganu da kuma rigingimu da ake samu a cikin masana'antar.

Wannan shi ne matsayin Kannywood wanda yanzu haka ana kan tantance mutane don kokarin kawo gyara.

Yaushe kake ganin kannywood za ta fara gogayya da ragowar sa'o'inta?

To duk abinda ake fada dai hasashe ne amma muna sa rai, don abubuwan da muke bukata dai na farko akwai yadda mu ma za mu samu harkar kasuwanci kamar sauran masana’antu idan ka yi fim za ka mayar da kudinka hankali kwance ba tare da ka yi asara ba, a qalla za ka ci riba, wannan shi ne abinda kowa yake fata.

Babbar bukatar ita ce samun kasuwannin da za a rika kai fim, shi ne mataki na farko da Kannywood take bukata a halin yanzu, don haka indai ba wadannan abubuwan ne suka samu ba, to abubuwa ba za su daidata ba.

Me yake assasa yawan ce-ce-ku-ce da baya karewa a kannywood?

Eh to matsalar ita ce mun maida kafafen sadarwar zamani wurin tonon asirinmu ko fadanmu. Idan ya zamana cewa kowa a na bibiyar halayen da yake a soshiyal midiya to ba za a zauna lafiya ba.

Shi ya a tsarin a wannan rajista, dole sai ka amince ba zai kara zuwa soshiyal midiya ya zubarwa da Kannywood mutunci ba. Saboda yawancin rigingimu a can ake yi tare da tattauna maganganun da ba su dace ba. Tafiya ce muke yi kara zube kuma ba tsari; duk abinda babu tsari, babu shugabanci to ko me zai faru ba za a iya cewa ga dalilinsa ba, amma yanzu idan akwai tsari da shugabanci to kowa dole ya bi tsarin shugabanci, idan ka ki hukuma tana da dama da za ta hukunta ka, sannan kungiya ma ta dauki mataki a kanka.

Menene kiranka ga sauran jarumai da kuma abokan aikinka?

Kirana gare su shi ne su daure su yi rajista saboda mafita muke nema gabadaya da kuma alfanunmu, mu yi wa harkar film mashiga da mafita ga duk wanda zai zo.

©HausaLoaded

Post a Comment

 
Top