Ya kuke ganin abun zai kasance a gaba?

Laraba 18 ga watan Satumba 2019, kotun zaben gwamna na jahar Kano a ta jingine hukunci kan karar da jam’iyyar PDP da dan takararta Abba Kabir Yusuf suka shigar.
Jam’iyyar PDP da dan takarar gwamnan ta wato Abba Kabir na kalubalantar kaddamar da Gwamna Abdullahi Ganduje a matsayin wanda ya lashe zaben da ya gudana na  23 ga watan Maris 2019.  Shugaban kotun zaben Justis Halima Shamaki, bayan sauraron jam’iyyun a kan lamarin ta bayyana cewa za a sanar masu da ranar yanke hukunci, inda tayi godiya ga jam’iyyun akan goyon bayan da suka bawa  kotun domin tayi adalci kan dukkan lamuran da ke gabanta.  Da farko, lauyan INEC, Ahmad Raji (SAN), ya roki kotun zaben da ta yi watsi da karar akan rashin fa'ida, a  yayin da yake gabatar da rubutaccen jawabansa na karshe,  ya kuma  bayyana cewa INEC bata yi kumbiya-kumbiya ba wajen gudanar da aikinta akan shaidun da ta gabatar a gaban kotun zaben ba.

Haka zalika a karshe alkalin gwamna Ganduje, Offiong Offiong (SAN), shima ya roki kotatun da ta yi watsi da karar wanda ke kalubalantar samun nasarar a yayin gabatar da rubutaccen jawabansa na karshe.

©HausaLoaded

Post a Comment

 
Top