Fitacciyar jaruman wasan kwaikwayon hausa ta Kannywood kuma mai taimakawa gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje ta musamman akan harkokin da suka shafi mata wato Rasheedat Adamu Abdullahi wacce aka fi sani da Rashida mai sa’a ta bayyana dalilin da yasa ta dan jingine aika-aikacen wasan kwaikwayo a gefe.

Rasheeda Adam wacce ta karanci kimiyyar siyasa(political science) a matakin digiri a hirar ta da wakilin jaridar Daily trust ta karshen mako ta bayyana cewa bayan wani film mai suna mujalla wanda mallakin jarumi Ali Nuhu ne dai ta yanke shawarar ta dan koma gefe don gudanar da harkokin kamfanin shirya fina-finai mallakinta domin ko a cewarta tun tuni dama tana da lasisi na shiryawa da fitar da fina-finai domin ko ta rigaya tayi ma kamfanin nata rajista wanda cike yake da kayan aiki na zamani


Da aka tambaye ta ko ta yaya ta tsunduma cikin harkokin siyasa sai ta kada baki tace:” A matsayina na yar jam’iyya, na kasance mai kare hakki game da kai koken mata yan jam’iyya wandanda basu morar romon dimokaradiyyar cikin jam’iyya wanda Allah cikin ikon ya sa mai girma Gwamna Ganduje ya dauko ni ya bani mukamin babbar mai taimaka mishi ta musamman a bangaren harkokin mata wadanda sune suka bada guddunawar akalla kaso saba’ in na kuri’un da suka kai gwamnati gaci”.
An tambayi jarumar kan cewar ko ta bar masana’antar film kenan, sai jarumar tace:” Har yanzu ina nan tsundum a masana’antar Kannywood, domin ko yanzu haka kamfanina na shirya fina-finai yana nan yana aiki. Duba da yanayin aikace-aikace da suke kaina a yanzu, kama daga ganawa da mutane daban-daban, karbar koke-koke, dama sauran ayyuka na ofishin da aka bani yasa na yanke shawarar ajiye harkar shirin film a gefe daya domin na rungumi aikin da nake yi ba kama hannun yaro”.
Jarumar ta jaddada cewa babban burinta a yanzu shine taga ta taimakawa gwamnatin Kano wajen ganin ta cimma muradunta na inganta rayuwar mata ta hanyar tallafa musu da kudade don sana’o’insu da kuma gyara harkar ilimi don yara su sami ingantaccen ilmi don samun rayuwa mai inganci.
Ta bayyana cewa lallai kwalliya tana biyan kudin sabulu a ayyukan da suke yi sannan kuma mata da yawa suna shigowa harkar siyasa ba kamar can da ba da ake yiwa mata dake siyasa wani irin kallo.”Kuma alhamdulillah matan dake shigowa suna kawo cigaba sosai a harkar tafiyar da gwamnatin”.
Daga karshe ta mika godiyar ta ga daukacin matan jihar Kano sannan tana kara basu tabbacin cewa gwamnatin Kano na nan na bakin kokarin ta wajen ganin ta inganta rayuwar su domin su kasance cikin farin ciki da walwala su da ahlinsu.


©HausaLoaded

Post a Comment

 
Top