Shugaban kungiyar IZALA Sheikh Abdullahi Bala Lau yayi kira ga 'yan uwa musulmi da suyi watsi da labarun karya da ke yaduwa a kafafen sadarwa na zamani cewa ya sauke babban Sakataren kungiyar Sheikh Kabiru Gombe. Sheikh Lau yace wannan zance ne na kage daga wasu bata gari wadanda basa tsoron Allah.
Shugaban ya kara da cewa idan munyi nasarar zakulo bata garin, zasu fuskanci shari'a, Kuma wannan ya nuna jajircewa da Sheikh Gombe ya keyi a fagen da'awa abin ya bawa ne kwarai.
Kungiyar Izala tana gamsuwa da dari bisa dari a ayyyukan da Sheikh Kabiru Gombe yake gudanarwa a kungiyar. Hakazilika a lokacin wasu ke kulla masa sharri. Maluman mu.
"Tsakanin mu da Sheikh Kabiru Gombe babu komi illa aminci da so da kauna, tare da addu'ar Allah ya karawa rayuwarsa albarka" Inji shi.
A karshe Sheikh Bala Lau yace baza a zuba ido wasu bata gari suna kulle kansu a dakuna suna yada labarin karya da sunan IZALA ba, akwai hanyar da muke bi kuma zamu kai ga binciko inda suke kuma zasu fiskanci hukunci insha Allah.
©HausaLoaded
Post a Comment