A yayin da sanatoci ke tantance daya daga cikin ministocin da shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya aike musu, Abdullahi Hassan daga jihar Nasarawa, wata sanata ta bayyanashi da kyakkyawa dalilin haka sauran sanatoci suka fashe da dariya.

Sanata Uche Lilian Ekwunife yayin da take wa ministan Abdullahi tambaya, tace a matsayinka na kyakkyawan matashi idan shugaban kasa yayi shawarar baka ministan harkokin mata lura da cewa an samu mata a matsayin ministocin mata a baya amma babu wani abin azo a gani da suka yi, wane abu zaka yi dan ganin cewa ka kawowa mata ci gaba ta hanyar samun mukamai da yun nasara a harkar zabe?

Abdullahi ya bata amsar cewa zai hada hannu da matar shugaban kasa, Hajiya A'isha Buhari dan ganin an samu nasarar ci gaban mata idan ya samu wannan mukami.

Post a Comment

 
Top