Kankana ta kasance daya daga cikin 'ya'yan itatuwa mafi shahara a doron kasa kuma mutane da dama su kan yi santi kwarai yayin kwankwadar ruwanta musamman wadanda kwayoyin halittun su masu bambance dandano ke aiki kwarai.
A yayin da kankana ta kasance cikin dangin itatuwa da ake kiransu 'ya'yan duma, 'ƙwallayen cikin da sun ƙunshi sunadarai masu tarin alfanu da kuma tasiri wajen inganta lafiyar jikin dan Adam.
Sai dai kash da yawan mutane su kan watsar da ƙwallon kankana a sakamakon rashin sanin muhimmancin su wajen inganta lafiyar su. Wadannan ƙwallaye da kankana ta kunsa suna da arzikin sunadarai da suka hadar da fatty acids, proteins, minerals (magnesium, poatssium, manganese, iron, zinc, phosphorus, copper), vitamin B (thiamine, niacin, folate) da kuma calories.
Bincike ya tabbatar da cewa, ana amfani da ƙwallayen kankana a matsayin abinci a yankunan nahiyyar Asia da kuma wasu yankunan daular Larabawa ta Tsakiya inda ake gasa su kuma kwadanta da ganyayyaki irin su Salad.
Ga dai wasu muhimman amfani da ƙwallayen kankana ke dasu a jikin dan Adam domin bunkasa lafiya:
1. Jikin dan Adam yana da matsananciyar bukatar dangin sunadaran amino acid kamar su arginine da lysine, sai dai kuma jikin ba ya iya samar dasu da kansa. Kwallayen kankana sun ƙunshi dangin sunadarin aminco acid kamar su tryptophan da glumatic acids.
Wannan sunadarai na da tasiri wajen bunkasar lafiyar zuciya da gudanar jini tare da inganta lafiyar ma'aurata musamman ni'ima, sha'awa da kuma karfin kuzari a yayin saduwa.
2. Kwallayen kankana sun kunshi sunadarin magnesium mai tasirin gaske wajen kara yalwar lafiyar zuciya, jini da kuma kariya ga cutar hawan jini da sauran cututtuka na zuciya.
Haka kuma tasirin sunadarin magnesium ya kan taimaka wajen rage kaifin ciwon suga.
3. Kara karfin mazakuta ga da namiji da kuma laushin kumatu na samuwa a sakamakon tasrin sunadarin lycopene da ƙwallayen kankana suka ƙunsa.
4. Dangin sunadarin Vitamin B da suka hadar da niacin, folate, thiamine, riboflavin, vitamin B6 da pantothenic acid da ƙwallayen kankana suka ƙunsa na da matukar tasiri wajen bunkasa garkuwar jiki da kuma ta ƙwaƙwalwa.
5. Kwallayen kankana na da matuƙar tasiri wajen dawo da kumari a jikin mutumin da ya farfado daga rashin lafiya.
Haka kuma ƙwallayen kankana na matuƙar ƙara kaifin basira.
©HausaLoaded
Post a Comment