Via:- Garkuwan Magabata

Diyar madugun Shi'a a Nigeria mai suna Suhaila Ibrahim Al-zakzaky wacce ke zaune a kasar waje, ta aikowa yan Shi'a masu biyar addinin ubanta (Shi'a) ido rufe tana umurtarsu da su ci gaba da fitowa zanga-zanga har a sako babanta.

Idan dai ba'a manta ba gwamnatin Nigeria ta ayyana sunan yan shi'a wadanda aka fi sani da Islamic Movement in Nigeria (IMN) a turance, saboda irin ta'addanci da tada fitina da suke yawan yi a cikin al'umma daga ciki harda kisan jami'an tsaron Nigeria tare da yiwa dokokin kasa karan tsaye.

Amma abin lura anan shine, Me yasa ita diyar al-zakzaky shuhaila ba zata dawo Nigeria ba don ta jagoranci zanga-zangar har a sako mahaifinta? A nawa gani duk yanda wani dan Shi'a ke son zakzaky ban zaton yafi diyarsa sonsa, idan kuma har wani alheri ne ake  samu idan anyi zanga-zangar free zakzaky ya kamata ace Suhaila ce a sahun gaba. Amma saboda toshewar basira irin ta dan Shi'a yana ganin idan ya mutu wurin cewa a saki zakzaky yayi shahada, to ya sani irin shahadar kuje ce yayi, babu lada kuma babu la'ada. Shin wai ayi shahada ta hanyar zakzaky wane addini ya karantas? Wane ilimi ya kware a kai a cikin ilmukka? Wane littafen addini ya rubuta?

Don haka kowa mutu wurin zanga-zangar free zakzaky yayi mussai wallahi. Ina kira ga yan Shi'a da suyi watsi da wannan hanya ta zakzaky ba komai a cikinta sai halaka tun anan duniya ballantana a gobe lahira.  Ku dawo cikin addini, kubi sunnah, kubi magabata ku zauna lafiya. Sa6anin haka halaka ta rayuwa da dukiya zata ta biyarku har abada.

©HausaLoaded

Post a Comment

 
Top