Daga Bangis Yakawada

Manyan Alkalai 47 Na Kotun Kare Hakkin Dan Adam Sun Ayyana Auren Jinsi A Matsayin Haramtacce

Wannan Kotu ita ce kotu mafi girma da karfi a duniya ta fuskar kare hakkin Dan Adam, kuma da wannan hukuncin da suka yanke, Kotun ta tabbatar da abubuwa kamar haka..

(1) Dukkanin kasashen duniya halastaccen aure shine na tsakanin Namiji da Mace

(2) Dukkanin wata Kotu da ke goyon bayan auren jinsi ta na matsayin kotu da ke yunkurin rushe Kyakkyawar alaka ta 'yan Adamtaka.

(3) An Amince da dokar hukuntawa da ladabtar da duk wadanda aka kama da aikata Auren Jinsi.

(4) Auren da duniya da dokoki suka amince da shi shine wanda ya kasance a tsakanin Namiji da Mace kawai.

(5) Ba a amince da duk wani yunkuri ko hankoro na yin auren jinsi a tsakanin mutane ba, dabi'a ce mummuna wacce ko dabbobi ba sa yi, dole a kyamace ta kuma a yake ta.

Alkalan 47 sun tabbatar da cewar ba 'yanci ba ne wani ya nemi keta alfarma da Allah ya yiwa jama'a ya shigo da batun auren jinsi a cikin su.
A sakamakon wannan hukuncin ya tabbata daga yanzu Luwadi da Madigo na matsayin haramun kuma abin ki a fadin duniya.

©HausaLoaded

Post a Comment

 
Top