Ba zan iya fitowa karuwa a fim ba-Hafsat Barauniya
Hafsat Idris wacce akafi sani da Hafsat Barauniya, Jaruma ce da Duniyar Kannywood ke ya yinta, wanda cikin kankanen lokaci sunanta ya karaɗe kowane lungu da saƙo na Arewacin Najeriya. Ta zamo Gwarzuwa a tsakanin jaruman da suka fafata a 2016.
Haifaffiyar garin Shagamu amma ‘yar asalin Jihar Kano, ta shimfiɗa kwarewarta a farfajiyar masana’antar fina-finan Hausa, gwana ce ta gwanaye wadda take yin kyau da zarar an ɗora mata kyamara. Wani ƙarin armashi game da ita shi ne yadda ba ta wasa da aikinta a matsayin Jaruma.
A wata tattaunawa da aka yi da ita kwanakin baya, jarumar ta ce ita fa ba zata iya fitowa a rol ɗin Karuwa ko kuma tantiriyar mace ba, kasancewar akwai waɗanda suke ganin yanayin da mutum ya fito a fim to haka ya ke a gaske. Sau da yawa ina faɗin cewar ba kowane rol zan iya fitowa ba.
Amma a wasu lokutan babu yadda mutum zai iya idan dai yana so ya zama jarumi, duk abin da aka zo maka da shi dole ka hau shi, tunda kowa yasan wasa ne. Amma ni dai ra’a yina bana son taka rawa mara kyau a fim, musamman wadda zai janwo ce-ce-ku-ce.
Hafsat Idris tayi fina-finai masu kyawun gaske, waɗanda suka samu karɓuwa a wurin ‘yan Kallo fiye da kowacce jaruma a 2016, da suka haɗa da; Ɓarauniya, Ɗan Kurma, Alkibla, Furuci, Haske Biyu, Ankon Biki, Biki Buduri, Ta Faru Ta Kare, Mu Zuba Mu Gani, ‘Yar Fim, Ibtila’i, da dai sauransu.
Haka Kuma Jaruma Hafsat Idris ta bukaci al’ummar Musulmi da Kirsitoci da su rungumi zaman lafiya da kaucewa rikice rikice, waɗanda babu abinda zasu amfanar sai rura wutar ƙiyayya da gaba a tsakanin ɓangarorin biyu. Hafsat ta faɗi hakane a wani faifan bidiyo da ta sanya a shafukanta na sada zumunta: Twitter da Instergram.
Inda ta ce Haƙiƙa ya kamata Musulmi da Kirista su ajiye banbancin ra’ayin Addini, su rungumi juna don samun zaman lafiya mai ɗorewa. Shi ne zai taimakemu mu cimma nasarar da muke fata shekaru aru-aru..
Ni Sa’ar Uwar ka Ce Inji Hadiza Gabon Ta Fada Ma Wani Da Yace Ta Tsufa
The post Ba zan iya fitowa karuwa a fim ba-Hafsat Barauniya appeared first on ArewaFresh.com™.
©Arewafresh
Post a Comment