Yau maudu’in zai yi magana ne akan yadda zamantakewa yake tsakanin matar uba, da yaran mijinta. Mafi aksarin mata na samun matsala a wannan gab’ar, ta rashin sanin hanyoyin da zasu bi don ganin sun samu zama ta fahimtar juna tsakanin su da yaran miji da suka tarar, walau suna tare da iyayensu ko an fita an barsu da su.

Bangaren Mata…


Ina son jan hankalinmu mu mata, a duk inda aka kira mace to ana nufin uwa ce ko da kuwa kin haifa ko baki haifa ba, wannan dabi’a ta kasancewa uwa tana tare dake sai dai rashin sanin yadda zaki fitar ko tafiyar da kanki da zai sa ki amsa wannan suna ta uwa.

A duk lokacin da kika shiga gida kika tarad da yara musamman wadanda suka fara girma da mallakar hankakin kansu ,to abu na farko shi ne karki bada wata kofa da zai sa su kalleki a matar uba kawai, ki bayar da kofofin da zasu kiraki da sunan uwa ta kowacce fuska.
Ta ya ya hakan zai kasance?

Hakan zai faru ne kawai ta hanyar kyautatawa a garesu.

Da kyautata zamantakewa tsakaninki da mahaifiyarsu idan kuna tare.

Idan ba kwa tare yi kokarin ganin ba ki gaza ba wurin yi musu abinda ya dace a matsayinki na uwa a garesu.
Ki basu dukkan taimako a lokacin da suka bukata a wurin mahaifinsu.

Karki bari su daukeki kishiya ko abokiyar gabansu.
Idan kuna tare da mahaifiyarsu, karki bayar da kofar da mahaifinsu zaiyi ta wulakanta ta a dalilinki.

Yi kokari ki zama mai fahimta da hangen nesa a duk lokacin da wani abu ya shiga tsananin ku.

Ki zama me yafiya a lokacin da sukayi miki ba daidai ba.

Karki zama me yawan kai korafi akansu wurin mahaifinsu.

Ki tayasu murna a lokacin da suka samu wani cigaba a rayuwa.

Ki zama me hakuri da sawa a rai cewar zaman ibada kika shigo yi.

Karki zama me kyashi akan abinda mahaifinsu ke yi musu.

Karki dauko matsalarki da mahaifiyarsu ya zama abinda zai hana muku zaman lafiya. Da sauransu.
Bangaren yara…

Wasu yaran kan zama kishoyoyi ko abokan gaba ga wacce mahaifinsu ya auro a matsayin abokiyar rayuwarsa, ko mahaifiyarsu tana gidan ko bata nan.

Irin hakan kan samo asaline wani lokaci daga mahaifiyarsu ta yadda kishi zai tunzurata tayi ta hada yaran da matar ubansu. Yayin da wani lokaci kuma a dalilin muzgunawa da mahaufinsu ke yiwa mahaifiyarsu saboda yayi sabon aure ke jawo yaran su dasa tsanar matar a cikin zukatan su.

Hanyoyin Da Yaran Za Su Bi Don Su Zauna Da Duk Wacce Mahaifinsu Ya Auro Lafiya

Abu na farko su sa a zuciyarsu cewar mahaifinsu yana da ikon karo mace har uku bayan mahaifiyarsu idan yana da iko kuma zaiyi adalci.

Su mutunta wacce mahaifinsu ya auro.

Idan mahaifiyarsu bata gidan kar su dauki hakan a matsayin abinda zai haifar musu da rashin zaman lafiya da wacce ta gidan.

Idan mahaifiyarsu tana gidan, kar su dauki rashin jituwar su ya zama dalilin tsanar matar ubansu.
Suyi kokarin nusar da mahaifiyarsu a lokacin da tado musu da wata matsala da ta shafeta da abokiyar zamanta.

Idan mahaifinsu nayin ba daidai ba a tsakaninsu, suna iya bashi shawarar da ta dace don samun wanduwar zaman lafiya a gidan.

Idan suka nemi wani abu basu samu ba wurin mahaifinsu kar su dora laifin akan matar uban.

Suna iya biyowa ta hannun matar mahaifinsu don neman wani abu wurin mahaifinsu.

Su mutunta ta kamar yadda zasu mutunta mahaifiyarsu.

Kar su zama masu kallon duk abinda tayi a matsayin kuskure.

Su zama masuyin uduri
Su san cewar abinda sukayi watarana shi yaran da suka haifa zasuyi.

Su zama masu kyautata lafazi wurin yi mata magana
A karshe su zama masu hakuri da biyyaya ga matar mahaifinsu.

Sannan mu sa ni a duk lokacin da mace ta shiga gidan miji ta nuna bata son yaransa to fa shi ma ba zai so ta ba. Haka suma yaran a duk lokacin da zasu nuna kiyyaya ga matar da mahaifinsu ya auro ta fa ba zasuyi haske a idonsa kuma suna nemawa mahaifiyarsu tsana da tsangwama ne a wurin mahaifinsu domin duk yadda tayi shi gani zaiyi ita ke zugasu ko tana gidan ko bata nan. Saboda haka muyi hakuri da juna a lokacin da zama ya hadamu.




© Sirrinrikemiji

Post a Comment

 
Top