Kin amincewar kotun ya biyo bayan korafin da lauyan INEC, Dayo Adedeji, ya yi yayin da aka kira mutumin a matsayin shaida na farko da masu kara suka kira domin ya fara gabatar da jawabi a gaban kotun a karar da jam'iyyar PDP da dan takarar ta na gwamna a Kano, Abba Kabir Yusuf, suka shigar.
Lauya Adedeji ya yi korafi ne a kan sunan shaidar da aka kira a gaban kotun, inda ya ce sunansa bai yi daidai da sunan da ke cikin takardar jerin sunayen shaidun da masu kara suka gabatar a gaban kotun ba.
"Mai girma, mai shari'a, abinda muke da shi a rubuce a sunan shaidar shine 'MD', amma kuma shi shaidar ya bayyana cewa sunansa Muhammad Buhari Sule, wanda hakan ya saba da abinda masu kara suka gabatar kuma suka rantse a kan sa. "Babu yadda za ai MD ya zama Muhammad Buhari Sule koda kuwa an dauki harufan farkon sunansa ne, a saboda haka ina kira ga wannan kotu mai albarka da ta hana wannan shaida yin magana," a cewar lauya Adedeji.
Da ya ke kalubalantar gabatar da shaidar, M. M Duru, lauyan gwamna Abdullahi Umar Ganduje, ya ce doka ta yarda a boye sunan shaida, amma tunda shi shaidar da kansa ya bayyana sunansa, ba zai ci moriyar dokar da ta amince da boye sunan shaida ba.
Sai dai, a martaninsa, lauyan jam'iyyar PDP, Eyitayo Fatogun, ya ce bisa dokar kotun sauraron korafin zabe ta shekarar 2011, ana boye sunan shaida ne domin bashi kariya.
A nata hukuncin, babbar alkaliyar kotun, Jastis Halima S. Muhammad, ta ce tunda masu kara na yin amfani da harufan farko na suna domin sakaya sunan shaidunsu, ta amince cewa 'MD' bai yi daidai da sunan Muhammad Buhari Sule ba, a saboda haka kotu ba zata karbi shaidarsa ba.
©HausaLoaded
Post a Comment