AMFANIN DOYA

Image result for yam

1-AN JINI DA CIWON ZUCIYA: 

Kamar yadda muka nuna a jadawalin baya cewa doya tana dauke da vitimin B6, mai yawa a cikitna wanda shike taimakawa wajen gurvata wata guba mai suna Homocyteine. Idan wannan guba tayi yawa a jini tana yin illa ga bututun da jinin yake bi, masu hawan jini da ciwon zuciya suna da yawan shi homocyteine a jininsu. Doya tana da pottasium da magnesium sune idan sukai qaranci a kan kamu da hawan jini. Mai hawan jini da ciwon zuciya zai iya amfani da doyar da aka gasa saboda tafi dafaffiya ko soyayya. Kuma ita ce magani. Mai waxannan cuta zai iya yawaita cin doya don amfana da vitamin B6, da ake samu a doya.

2-BASIR (PILE)

Doya na dauke da fibre mai rigakafin basir amman idan ana son inganta amfanin doya wajen cutar sai a cita da ganye kamar latas, kebeji, alayyahu da zogale. Ana so a gas doya idan za'a domin tafi dafaffiya kuma ita ke magani.

3-CIWON SUGA (Diabetes)

Wajen ciwon suga doya na da fibre mai daidaita sugar da ke shiga cikin jini sannan tana da "magnesium" da "manganese" masu taimakawa jiki wajen amfani da suga. Cin doya yafi cin shinkafa 'yar waje domin mutum yana samun kariya daga cututtuka musamman wadda aka gasa.
4-RAGE QIBA (Slimming):

Idan mutum yana da qiba kuma yana so ya rage ta to ya yawaita cin doya saboda sinadarin "fibre" kuma cin alkama, dawa, gero, zogale, acca da lamsir suna da sunadarin "fibre" fiye da doya. Suma suna taimakawa sosai kuma mai son rage qiba ya yawaita cin doyar da aka gasa.
FADAKARWA:

Haqiqa kamar yadda muka faxa a baya game da cutuka da magunguna waxanda suke maganin waxannan cututtuka watau na Asibiti ko waxanda suke a cikin abincinmu da muke ci da yadda ya kamata mu yi amfani da ko dai nau'in abincin ko wasu tsirrai, domin kuwa mu gani yadda suka amfani wajen wasu cutuka.

Allah (S.W.T) ya kawo cututtuka da kuma maganinsu saboda haka nake so in sanar da ku cewa akwai wani maganin mai xauke da sinadarai daban-daban a cikin sa masu matuqar amfani wajen magance cutuka daban-daban Insha – Allahu.


Sirrin Rike Miji


© Sirrinrikemiji

Post a Comment

 
Top