YA jiya jumma’a ne, Hassan Giggs, produsa kuma jarumi a masa’anatar fim ta Kannywood ya tallafa wa da fiye da almajirai 1,000 da kayayaki da aka kiyasta ya kai na Miliyoyin Nairori a garin Kano, babban makasudin bayar da kayayyakin shi ne na taimaka musu don kare su daga sanyin hunturu da ake fuskanta a halin yanzu a arewacin kasar nan.jaridar leadership ayau na ruwaito.

Jarumin dai ya dade yana aikin tallafawa marasa galihu, ya kuma kadu ne da halin da almajirai suka shiga musamman a wannna lokaci na sanyi wanda a haka ne kuma zaka gansu suna yawo do neman abin da za su ci a lungunar yankin arewacin kasar nan. Akan haka ya kuma yi kira na musamnan ga iyaye na su rungumi hakkin tarbiyar yaransu don su kasance yara na gari da za a yi alfahari dasu a cikin al’umma, ta haka kuma za su bayar da gudumawarsu a ci gaban al’ummar da suke ciki.

Giggs ya kuma kara da cewa, “Babban abin da ya karfafamu na raba wa almajiran kayayyakin shi ne na ganin yawancinsu suna rayuwa ne a ciki yanayi mai ban tausayi musamman a wannan lokacin da ake fuskantar matsananciyar sanyi na hunturu. Na lura da cewa, yawancinsu basu da kayayyakin da zai kare su daga matsananciyar sanyi a da ke yi a halin yanzu wasu ma basu da takalmin da za su sa, lallai rayuwua a haka yana da wahala kwarai da gaske. “Kana sane kuma da yawancin yaran basu da wurin kwana mai kayau da zai iya kare musu sanyi don haka wadannan kayan sanyi zai yi matukar taimaka musu a wannan yanayi na hunturu; a kana haka ne na nemi abokina mai suna Ali Jita muka hada hannu don ganin yadda zamu taimaka wa wadannan yaran da dan abin da muke dashi” inji shi.

Ya kuma bukaci iyaye su tsayu wajen ba yaransu tarbiya yada ya kama mai makon tura su birane da sunan neman ilimin addini.

©HausaLoaded

Post a Comment

 
Top