Daya daga cikin masu shirya fina-finai a masana’antar Kannywood, Mustapha Ahmad wanda a ka fi sa ni da Alhaji Sheshe, ya tabbatar da cewa ba shi da wa ta matsala da kowa a masana’antar kannywood.norhflix na ruwaito.

Mustapha Ahmad, ya bayyana hakan ne lokacin da su ke wata tattaunawa da wakilin mu jaridar mu ta Northflix dangane da ci gaban, rikice-rikicen da kuma kalu balen da masana'antar Kannywood ta fuskanta a shekarar da ta gabata.

Wakilin namu ya tambayi mashiryin fim din cewa ko ya ka ke kallon masana'antar nan gaba?

Sai ya ce " Gaskiya akwai alheri da cigaba a Kannywood nan gaba amma gaskiya shekarar (2019) da ta gabata mun samu kalubale sosai, wanda har sai da ya sa masana’antar ta tsaya chak. Wadannan kalubalen su ne kasuwancin fim da kuma masu satar fasaha ma'ana masu tura fina-finai ta komfiyuta wato ‘yan downloading, sai mutun ya sa ka manyan kudade ya yi fim mai kyau da ma'ana sai ka ga masu tura fim a waya suna turawa mutane kyauta, dan kuwa Naira (20) ko (50) su ke karba idan sun turawa mutane fim kamar kyauta ne a kan yadda a ka yi fim din".

Ya ka ke ganin rayuwar duk wani dan fim ko mai shirya fim nan gaba idan bai tashi ya yi ilimi a kan sana'ar sa ba ganin yadda masu hannu da shuni su ke sa ‘ya’yan su a makarantun koyan shirya fim?

Sai ya amsa da cewa "Toh ai kullum cikin haka mu ke ko da yaushe muna kokarin karo ilimi a kan abun da bamu sa ni ba domin mu kawo sabon abu a cikin ayyukan mu, muna zuwa sanin makamar aiki da kuma bita akan harkokin fim, domin yanzu haka da yawan mu muna da dshaidar karatun Diploma a kan harkar fim wanda mu kayi a jami'ar Maitama Sule dake Kano. Kuma Insha Allahu zamu samu ci gaba sosai a Kannywood nan gaba kadan." Inji mashiryin fim din.

Ya kuma Kara mana da cewa” Shi ya na nan ya na shiri wajen kawo fina-finai masu tsafta da ma'ana kamar yadda ya saba, kuma Kayataccen fim din nan mai suna (Taqaddama) a matsayin zakaran fim din sa a cikin fina-finan da ya shirya, kuma fim din shiri ne wanda zai rika maimaita kan sa kuma ba za a daina yayin sa ba saboda ilimin da fadakarwar da sfim din ya kunsa”. Inji Mustapha.

Daga karshe ya yi wa duk wani abokin aikin sa da yan kallo fatan alheri tare da yi wa kowa addu'ar sa'a a wannan sabuwar shekarar da muka shiga.

©HausaLoaded

Post a Comment

 
Top