Me gudanar da shafin masoyan tauraron fina-finan Hausa, Ali Nuhu na dandalin Twitter ya bayyana labarin yanda aka samar da shafin da kuma magance matsalar cewa Alin yana da girman kai.

A cikin labarin da ya bayar yace mafiya yawan masu cewa Alin nada girman kai mata ne saidai Alin na kaffa-kaffa da sune saboda irin aniyar da wasu daga cikin su ke nufar jarumai da ita.

Yace, koda shi dake gudanar da wannan shafi yakan samu sakwanni marasa kan gado da wasu matan ke aikomai inda sukan ce zasu iyayin koma menene dan a hadasu da Ali Nuhu.





Post a Comment

 
Top