Wannan abin baƙin cikin ya faru ne a daren Lahadi, 28 ga Disamba, 2019.
Ruƙayya, wadda aka fi sani da Samira Saje, ta shaida wa mujallar Fim cewar, "A wannan rana da kai na na kulle shagon da misalin ƙarfe 9 na dare, don da ma tun da na buɗe shagon ni ke buɗewa kuma ni ke kullewa.
"A lokacin ma masu aiki na duk sun tafi hutun Kirsimeti, yaya na kuma da ma shi ne manaja, ba shi da lafiya, kusan kwana uku bai fito ba, shi kaɗai na ke bari a gida na tafi shagon."
"Da safiyar Litinin, 29 ga Disamba, 2019 na fito da misalin ƙarfe 10 na buɗe shagon sai na ga an rubuta ‘I love you Samira’ a kan teburin kashiya ta, sai na ce, 'A’a, jiya fa ni na kulle shagon nan da kai na, ya aka yi aka zo aka rubuta wannan, kuma ni ba 'birthday' na ba ballantana a ce 'surprise' ne, kuma wa ke da makullan?'
"Ban kuma ɗaga kai na na kalli kayan da ke cikin wurin ba, sai na shiga ɗakin gyaran gashi.
"Ina shiga, sai na ga an buɗe 'window' an ɗaura igiya. Na fara salati.
"Da gudu na fito.
"Kuma abin da ya ba ni mamaki, ta ƙofa aka shiga, kayan su ka fitar ta 'window' tunda shagon a sama ya ke.
"Sun yi amfani da wayar janareto na ne a wurin sauke kayan, sun ƙulla shi a jikin 'window' ɗin. Kuma dukkan makullai na na hannu.
"Sai dai sakaci ɗaya na yi: tun da na kama wurin ban canza makullan ba, domin makullan da na samu a wurin su ne.
"Kuma tun kafin in buɗe wurin, ina shirin buɗewa aka shiga aka sace mani kayan sama da N300,000. Wannan ma shi ne ya kawo tsaiko, ya sa ban buɗe shagon da wuri ba.
"Ga shi yanzu kayan N1,600,000 aka kwashe mani. Na gano haka ne ta 'record book' ɗin mu da kuma risit.”
Samira ta ce kayan da ɓarayin su ka ɗiba sun haɗa da talabijin, takalma, agoguna masu tsada waɗanda farashin su ya kama daga N25,000 zuwa N35,000 ko N45,000 kowanne ɗaya, da huluna masu tsada da kayan mata da su ka haɗa da jakunkuna uku da takalma 15, ‘yan kunnaye ma ko ɗaya ba su bari ba, da sauran abubuwa.
Mutum na farko da aka kama shi ne maigadin wurin da shagunan su ke, don shi ne aka fara zarga.
Ta ce, "Shi kuma ya faɗi mutanen da su ka shiga gidan a ranar, kuma su ne na ƙarshe da su ka fita; duk an kama su."
Yanzu haka maganar ta na ofishin 'yansanda na 'State CID', ana bincike.
©HausaLoaded
Post a Comment
Click to see the code!
To insert emoticon you must added at least one space before the code.