Jaruma Hadiza Muhammad ta bayyana hakan ne yayın da aka gudanar da taron karrama jaruman Kannywood na Bon Award wanda ya gudana a jihar Kano a kwanakin baya.
Hadiza ta ce " wasu dalilai ne kawai ya kawo tsaiko na rashin shiga fim din Nollywood.
duk inda al'umma ta ke a rabe to akwai wasu abubuwa da ba za a iya cin musu ba, amma idan a ka ce an samu hadin kai to babu shakka za'a cimma nasarar da a ke bukata a kowane bangare".
Ta kara da cewa "Arewacin Nijeriya muke gudanar da sana'ar mu ta fim, su kuma suna kudancin kasar nan su na gudanar da sana'ar su ta fim kuma su na amfani da harshen turanсi da kuma yarensu wanda hakan akwai banbancin yare da al'ada a tsakanin su. Hada kai da mu ke yi a halin yanzu na fina-finai ya na da amfani matuka domin ta hakan ne zamu yi fim ya kuma je inda ba a tsammani a fadin duniyar nan.
Ba wani abu ba ne in mun hadu da jaruman kudancin kasar nan a harkar fim, domin ta wannan hanyar ce za mu iya karuwa a tsakanin juna. Saboda haka har idan mun hadu da jaruman kudancin kasar nan mun yi cudanya da juna zamu samu cigaba kuma fim din mu zai je inda ba'a tsammani". In ji Jarumar
Jarumar ta kuma rufe jawabin ta ne da cewar "ba wani abu bane samun damar, kawai dai wasu dalilai ne suka hana ni, saboda a kwanakin baya an yi mun tayi amma ban samu damar zuwa ba don na yi fim din Nollywood kuma batun kasuwan cin mu na Kannywood kuwa, ba wani abu bane yake kawo mana tsaiko, illa kawai masu harkar tura fim a waya wato 'yan downloading ne suke mayar da hannun agogo baya a harkar masana'antun Kannywood". A cewar Hadiza Muhammad.
©HausaLoaded
Post a Comment