Jarumar, wadda kuma furodusa ce, ta bayyana hakan ne a lokacin tattaunawar ta da mujallar Fim a Kano.
Khadija, wadda da yawa su ke yi mata kallon mace mai aji a cikin matan da su ke harkar fim, ta ce, "Ita harkar fim sana'a ce a waje na, domin a fim za ka haɗu da jama'a da za ku zama 'yan'uwa kuma abokan sana'a.
"Don idan ka shigo harkar fim kun zama ɗaya da masu yin harkar, ku yi tafiya tare, ku zauna waje ɗaya, ba ka da wanda ya fi su.
"Don haka ko da wani zai kalli harkar fim ba a matsayin sana'a ba, to ni dai sana'a ce a waje na."
Ta ƙara da cewa "Yanayin harkar fim ya na da ban-sha'awa kuma ya na da 'yar wahala, domin kafin ka fara harkar fim ka na rayuwa kai kaɗai ne, za ka shiga kasuwa, ka je gidan biki, da sauran mu'amaloli babu mai sa maka ido, babu ruwan ka da kowa.
"Amma yanzu ina tafiya a kan hanya, wasu ma ba su san suna na ba, da yake su na gani na a fim sai su rinƙa faɗar ga 'yar fim can.
"To waɗannan abubuwan duk su na faruwa. Don haka akwai ƙalubale a rayuwar ɗan fim."
Daga ƙarshe, Khadija ta yi kira ga 'yan fim da su haɗe kan su tare da kare mutuncin sana'ar su.
©HausaLoaded
Post a Comment