*SHAWARA GA MATA MASU HANKALIN DA TUNANIN YA KAMATA*


MAGANA KAN KARA AURE ( KISHIYA )


mafi yawanci Mata 90% na shiga cikin damuwa lokaci DA mijinki ke Neman Aure KO kuma zai Kara Aure saboda baki San wacce zai aura ba.

Dole ki damu domin akwai zafi sosai, sai dai yana DA kyau ki tuna Allah ( SWT ) shi yayi umarni Kara Aure kuma ya gargadi mazaje idan ba zakuyi adalci ba Kada Ku Kara Aure domin ranar kiyama zaka tashi DA barin jiki ya shanye, Allah ya kyauta.


*idan har ke mai tunani ce Bai kamata ki juyawa mijinki baya ba saboda zai Kara aure, musamman wasu matan sai su daina *wanka *kwalliya *tsafta DA duk wasu abubuwan DA ya kamata wanna shine kuskure na farko DA kikayi, domin namiji ba'a masa dole, Kada ki taba yaudara kanki wata Rana ba za'a miki kishiya ba, amma wacece ita kishiya, dame Zatazo gidan.


*HANYAR MAGANIN DAMUWA TA KISHIYA*


* koma zuwa ga Allah ( ma'ana ) Addu'a ya Allah idan alkhari ce ka kawo ta mu zauna lafiya, idan ba alkhari bace sauya masa. Kin zauna lafiya sai Allah yasa natsuwa cikin zuciyar ki.


* sadaka na kauda masifa yawaita sadaka.

* kyautatawa mai gida, Kada ki taba sauyawa lokaci DA yace zai Kara Aure domin zai ji karfi gwiwa ne lokaci DA kike nuna bakiso.

* gyaran jiki, wata tun ranar farko rabon ta DA gyaran jiki, ki dinga wadannan zai Kara miki kyau Wurin sa.


*Sanna mai gida, idan zakayi Aure Kada ka taba gayama amarya kuskure uwargida domin zata raina ta sai a kiyaye sai a zauna zaman lafiya.


Sirrin rike miji


© Sirrinrikemiji

Post a Comment

 
Top