Fitaccen jarumin fina-finan Indiya Shah Rukh Khan na daya daga cikin jaruman fina-finai na kasashen duniya 15 da Sudaiyya ta karrama su da wata lambar yabo ta Joy Excellence Award a wani biki a ranar Litinin.
Shah Rukh Khan ya wallafa sakon godiyarsa ga Saudiyya a shafinsa na Twitter tare da sanya hotunan yadda bikin ya gudana.
Da ya zo jawabin godiya yayin karramawar, jarumin ya fara ne da: 'Bismillah al-rahman al-rahim,' wato 'Da sunan Allah mai Rahama mai jin kai'

Sannan sai ya gayar da taro da yi musu sallama irin ta musulunci. Duk da cewa Khan musulmi ne, ya kasance baya nuna bambanci ga sauran addinai don matarsa Gauri Khan mabiyiyar addinin Hindu ne kuma sun shafe shekara 28 suna tare.
King Khan kamar yadda aka fi sanin sa da shi ya kuma yi magana a kan ci gaban da Saudiyya za ta samu nan gaba duba da yadda ta bude gidajen kallo na sinima, bayan da yarima mai jiran gado ya dage haramcin da da aka sanya.
"Mun ta yi magana a kan karamcin da aka yi mana, da girmamawa da soyayya .... kuma ma dai wannan ita ce tafiya ta farko da muka yi zuwa kasar ta Saudiyya," a cewarsa kamar yadda shafin intanet na National ya ruwaito.
Ya kara da cewa "Inshallah, za mu jira cike da doki saboda an bude gidajen kallo anan Saudiyya. Akwai labarai da dama da za a fada, kuma mu a matsayinmu za mu taimaka da duk abin da za mu iya."
Sauran wadanda aka karrama sun hada da wata fitacciyar jarumar kasar Masar Ragaa El Gedawy da jarumin Game of Thrones da Aquaman Jason Momoa.
Jason Momoa ya ce ya fada cikin kaunar Saudiyya dumu-dumu tun karon farko da ya je kasar a shekarar 2017.
Ya kuma kara bayani kan yadda ya taka rawa a sauyi da aka samu a Saudiyya: "Abu ne mai kyau a ga sauyin da aka samu ko don al'umma mai tasowa"
Shi ma tauraron fim na Belgium Jean-Claude Van Damme da aka karrama ya ce ya ji dadi da aka ba shi lambar yabo mai siffar mikiya mai ruwan gwal.
Baya ga wadannan akwai kuma fitaccen jarumin fina-finai dan kasar Hong Kong wato Jackie Chan da shi ma ya karbi lambar karramar, sannan da hawansa kan dandamali sai ya ce "salam alaikum".
"Na san da yawanku sun sanni. Na shafe shekara 59 ian yin fim. Wannan ne karo na farko da na zo Saudiyya, gaskiya babbar kasa ce. Ina fatan na sake dawowa da tawagata ta shirya fim nan kusa."


©HausaLoaded

Post a Comment

 
Top