Samun nutsuwar ruhi da abokiyar zama ba ya yiwuwa sai ta hanyar auratayya, domin idan ta fuskar fasikanci ne ake zaune da juna wannan nutsuwar ruhi har abada ba za ta taba samuwa ba, wannan kuwa abu ne sananne da dabi’ar halittar mutum da ilimi suka gaskata. Saboda haka duk wanda zai yi aure ya tuna ko ta tuna cewa, za ta yi aure ne da wanda za su zauna domin gina rayuwa maras iyaka da gina gida salihi.
Amma tambaya a nan ita ce: wanne mutum ne za mu zaba domin wannan rayuwa da samun nutsuwa da soyayya da kuma tausasawa juna?
Ba a son a samu shakuwa sosai sai da wanda za ku yi aure da shi, saboda haka irin soyayyar da ake yi ta al’adun da suka shigo cikin al’ummar Hausa musamman daga yammacin duniya ba ta da kyau ko da aure za a yi ballantana da yawa ba ma a kai wa ga auren.
Sau da yawa takan kai ga aikata haram wanda zai yi tasiri a kan saurayi da budurwa har karshen rayuwarsu, kuma sau da yawa rayuwar ‘yan mata ta lalace sakamakon irin wadannan miyagun al’adu.
Sau da yawa mace mai saukin hali da samari sukan iya shawo kanta ta hanyoyi daban-daban wani lokaci ma har wani shakiyyi yakan ce da ita: Idan kika yarda da ni muka kwanta to lallai zan aure ki. Irin wannan da yake son sha’awa ne ba na Allah da Annabi ba, da zaran ya santa a ‘ya mace, sai ya yi wurgi da ita ba ma za ta san cewa mugu ba ne mai tsananin wulakanci sai idan ta samu cikin dan shege ta wannan mummunar hanya, a lokacin ne za ta san cewa baya kaunarta koda kwayar zarra.
Sau da yawa a kasashen duniya da kasashenmu ‘yan mata sukan kashe kansu saboda wannan mummunan hali da mayaudaran samari suka jefa
su a ciki, rayuwa ta gurbace wusu suka ko ma abin tausayi ko kuma suka gudu daga garuruwansu, ko ma suka haifi dan amma suka yarda shi a kwararo suka gudu.
Da yawa mata suna da saukin hali shi ya sa suka yaudaru da wuri, wasu kuma kwadayi ne yakan kai su ga fadawa irin wannan mummunan hali, don haka yana kan iyaye da su rika sanin mene ne ‘yarsu take yi a waje, kuma da wadanne irin kawaye ne take yin mu��amala, sannan kuma su waye suke zuwa zance wajen ta da sunan suna son aurenta.
Bayin Allah in kun yi aure ku raba ayyukan kwanaki da suke hawan kanku a matsayinku na masu auratayya. Kada mace ta yi wa miji gorin satifiket ko wata shaida ta ilimi ko wani abin da ka iya nuna gori a kansa haka nan shi ma haka. Kada ki sa ran sai an yi miki abu irin na kawarki, ya kamata ki kula da iyakar mijinki da godewa, domin rashin hakan kan iya karya masa karfin yi miki hidima.
Kada a yi wa juna nasiha a gaban yara ko mutane, a bari sai hankali ya kwanta an huta, sannan sai a yi wa juna nasiha cikin wasa da dariya hakan yakan fi tasiri ga ma’aurata. A jawo kaunar juna da aiki ba da magani ba ko barazana. Kowa ya yi mu’amala da abokin zama da tausasawa ba da tsanantawa ba. Kada mace ta sake ta bayar da fuska sai ga mijinta, haka ma kada ta sake ta tsananta wa mijinta, kuma ta sani kullum dole ta bujuro da kanta ga mijinta. Bawa ‘ya’ya isasshen lokaci da
zama da su da hira da su da kuma tunatar da su kan rayuwa.
Girmama na gaba kamar uwar miji ko uwar mata yana daga kyawun zamantakewa da kargonta, wato girmama iyayen juna.
Bawa juna isasshen lokaci na tattaunawa da hira da warware matsalarsu.
Wani lokaci matar mutum ta kan cutar da shi wajan ta taimaka masa ko makamancin haka, wannan wani abin yafewa ne da kauda kai, saboda yana faruwa ne daga kauna da son taimakawa daga mata
© Sirrinrikemiji
Post a Comment