Rahoto daga legithausa.
Wani sabon bincike ya nuna cewa manoma sun fi sauran gama garin jama'a yin jima'i - saboda bincike ya nuna cewa kashi daya bisa uku na manoma suna jima'i akalla sau daya a rana.
A cewar rahoton New York Post, kashi 67% na manoma sun bayyana cewa sun yawan yin jima'ai. Binciken wani mai kera yar tsana, Lelo, ya laburta.
Wata kwararriyar masaniya ilimin jima'i, Kate Moyle, ya ce dalilin hakan shine manoma sun fi sauran mazauna birni koshin lafiya da karfin jiki.
Kate Moyle ta bayyanawa jaridar UK Mirror cewa: "Ko a tsakanin mutane akwai banbanci sosai, ya kamata mu lura da banbancin tsakanin mutane kuma hakan na da alaka da rayuwar aurensu."
"Amma, za'a mu iya kiyasi kan wasu abubuwa, irin aikin karfin da wasu ma'aikata irin manoma keyi na taimakawa sabanin ma'aikacin ofis."
Rahoton ya kara da cewa bayan manoma, sai masu zanen gini inda kashi 21% ke jima'i sau daya a rana, sannan masu gyaran gashi inda kashi 17% ke yi a rana.
A cikin binciken mutane 2000 da Lelo ya yi, ya gane shekar Yan jarida ne masu karancin jima'i da iyalansu.
A bangare guda, Masu shan shayi akai-akai sun fi lafiyan kwakwalwa - hakan yana nuna sun fi lafiyar rayuwa - fiye da maras shan shayi, sabon binciken kasar Singapore ya bayyana.
Farfesa Feng Lei, kwararren malamin lafiyar kwakwalwa a tsangayar ilimin magani na Yong Loo dake jami'ar kasa ta Singapore ya bayyana cewa shan shayi na da muhimmanci ga lafiyar kwakwalwa.
©HausaLoaded
Post a Comment