Duk A Cikin Shirin 'Yan Fim da Finafinai, Wanda Jaridar Dimokuradiyya Ke Daukar Nauyi

Wakilinmu Mukhtar Yakubu Kano

A yanzu dai za a iya cewa babu wata jaruma a cikin sabbin jarumai da ta kai Zulaihat Ibrahim wadda aka fi sani da Zpreety suna da kuma tashe, ba don komai ba sai don 'yan gajerun finafinan da take yi na barkwanci tana turawa a Soshiyal midiya.

baya ga haka a yanzu tana da kusanci da babban jarumi Adam A Zango, don haka ne ake yi mata kallon jarumar da take tashe a wannan lokacin.

Wannan yasa wakilin mu ya yi mata tambaya a kan kowanne shiri ta yi wa rayuwar ta nan gaba musamman idan ta duba yanayin 'yan fim da suka yi tashe kafin ta zo wadanda a yanzu wasu sun bar harkar, wasu kuma suna cikin ta amma ko tuna su ba a yi?

Sai ta ce " To abu na farko dai shi ne tsare mutunci da kuma nuna tsoron Allah, a duk in da ka samu kan ka shi ne babban tanadin da ya kamata dan fim ya yi wa kan sa.

Kuma ni a yadda na dauki harkar fim na zo ne don na isar da sako domin mutane su fahimta Kuma su kara.

Kada  mace ta shigo harkar fim da tunanin tana so ta yi suna don ko ba ka nemi ka yi sunan ba idan lokacin ya zo ka yi sunan za ka yi don haka mace ta yi abin da ya dace ba wai ta zubar wa kan ta da mutumci ba , don haka tsare mutunci da sanin ya kamata shi ne zai sa ki samu matsayin da kike nema.

Ta ci gaba da cewa " duk da ina cikin harkar fim a yanzu  ba wai na shiga da niyyar babu aure a gaba na ba, duk lokacin da Allah ya kawo wanda muka fahimci juna  da shi  sai kawai mu yi aure da shi domin shi aure sunnah ce Kuma da iyayen mu ba su yi ba to ba za a same mu ba don haka su ma burin su kenan su ga mun yi auren.

Daga karshe ta yi kira ga mata 'yan fim da cewar' mu rinka kula da wadanda suke zuwa wajen mu da sunan za su aure mu, domin akwai 'yan yaudara sosai , don haka mata a nutsu a rinka kula da maza sasai.

©HausaLoaded

Post a Comment

 
Top