Fitacciyar jarumar finafinan Hausa Fatima Isah Muhammad wadda aka fi sani da Teemah makamashi ta bayyana irin wahalar da ta sha kafin Allah ya kaita matsayin da take a yanzu na daya daga cikin shahararru a masana’antar Kannywood.

Teemah makamashi ta ce ta sha bakar wahala kafin ta shiga harkar fim da kuma matsayin da take kai a yanzu.

Haifaffiyar garin Yola, da ta yi furamare da sakandire duk a Adamawa, kafin ta wuce jami’ar Maiduguri ta kammala karatun difloma bangaren koyon harshen larabci.

Dangane da yadda ta samu kanta a harkar fim, Teemah ta ce, “Sha’awa ce ta sa na shigo harkar kuma na samu shiga ne ta hanyar marubucin labarin fim Abdulkarim Papalaje. Shi ne ya rika gabatar da ni cikin su, da haka har na samu shiga kuma irin wannan fadi tashin na ganin na karbu a wajen su ne na sha wahala sosai. To amm da ya ke an ce mahakurci mawadaci, yanzu sai dai labari, don kuwa na sha gwagwarmaya sosai.

Ta ce, “a baya na sha fita aiki wasu su biya ni wasu kuma ba sa biya na, amma yanzu da lokaci ya zo ana bani labarin fim din idan zan karanta kafin na zo aiki an fara biya na kudi, don haka ma sai abin yake bani mamaki. A baya ka yi aikin a hana ka kudin ka, ko a baka da guntu-guntu, wasu ma da ba sa tsoron Allah sai ka yi aikin su hana ka kudin, amma yanzu ya wuce sai dai labari.

Dangane da irin nasarorin da ta samu kuma cewa ta yi “Babbar nasarar da na samu ita ce arzikin jama’a, domin kuwa na shiga wurare da dama wanda ba don arzikin jama’a da na samu a fim ba to ba zan iya shiga ba, don haka na tsinci kaina a inda ban taba zato ba, kuma fim ne ya kaini.

©HausaLoaded

Post a Comment

 
Top