Duk A Cikin Shirin Fina-Finai, Wanda Jaridar Dimokuradiyya, Ke Daukar Nauyi

Wakilinmu Mukhtar Yakubu Kano

Babbar matsalar da muke fuskanta ita ce ana son mu Kuma ana zagin mu , don haka mata 'yan fim muke samun matsala a wajen neman auren mu da ma shi kan sa zaman auren.

Tsohuwar jaruma Zakiyya Ibrahim a lokacin da take yi wa wakilin mu bayani dangane da mutuwar auren ta bayan sun yi zama da mijin nata har tsawon shekara uku kafin ya sake ta.

Ta kara da cewa "ni da miji na aure muka yi na soyayya amma daga baya abokan sa suka rinka kai masa maganganu iri iri a kai na  wai 'yan fim ba su da kamun kai Kuma ba sa zaman aure, tun ba ya yarda har ya zo ya fara yarda da maganar ta su ya rinka zargi na da haka muka fara samun matsaloli da shi har muka rabu.

Mun tambaye ta shi mijin nata mazaunin Kano ne? Sai ta ce ' Dan Kano ne, amma a Saudiyya ya ke da zama shi da matar sa uwar gidan sai dai in ya samu hutu ya zo ya yi kamar kwana 40 Kuma nima a zaman mu da shi ya  kaini na yi shekara a can kafin na dawo, muna zaman lafiya da shi yana so na ina son sa amma dai kamar yadda na fada maka munafukai ne suka raba mu'.

Ko a zaman Ku da shi kun samu karuwa? Sai ta ce, To ban samu haihuwa ba amma dai sau uku ina samun juna biyu yana zubewa.'

Ko akwai wani kira da za ki yi ga jama'a game da auren 'yan fim?

kiran da zan yi mutane su daina yi mana kallon 'yan iska muna da mutuncin kamar sauran mutane idan ma an ce akwai bata gari a cikin mu ai ba duka aka zama daya ba suma sauran mata ai ba dukkan su ne na gari ba don haka a rinka kyautata mana zato".

Me za Ku Ce?

©HausaLoaded

Post a Comment

 
Top