Ali Nuhu Yafi Daraktoci Da Yawa Iya Bada Umurni – Abubakar Bashir Maishadda

Gajeriyar tattaunawa da Northflix ta yi da furodusa Abubakar Bashir Maishadda

Ya kake kallon masana’antar fim a halin yanzu?

Toh, Alhamdulillah. Hakika masana’antar sai da mu gode wa Allah. Domin akwai dimbin mutane, wadanda aka sani, da wadanda ba a sani ba. Kuma musamman  a yanzu da masana’antar ta hau kan wani layi wanda in sha Allah zai haifar mata da da mai ido. Ma’ana, za ka yi fim, ka kai sinimi, dubunnan mutane su zo kalla. Daga sinima kuma ana bawa gidajen talabijin, sai kuma kafofin yanar gizo, misali irin Northflid, sannan mutum zai iya buga CD ya sayar a kasuwa. Mu dai babu abinda za mu ce game da masana’antar fim zai godiya, domin ta dauki wani layi na cigaba.

Menene sirrin kyakkyawar dangantakarka da Ali Nuhu?

Maddala da wannan tambaya. Ali Nuhu mutum ne mai matukar muhimmanci a wannan masana’anta. Domin bayan fitowa a matsayin jarumi da yake, ni gamsu cewa babu mutumin da yake min aiki mai kyau a fim din kamar shi.

Tun daga lokacin da mu ka yi fim din Mariya, na tabbatar da cewea shi ne mutumin da ya kamata mu ci gaba da aiki da shi. Mun yi Mujadala, Hafiz, Hauwa Kulu da Sareena. Babban dalili shi ne, Ali Nuhu yakan tsaya tsayin daka ya yi aiki tukuru don tabbatar da ganin an fitar da ingantaccen fim, wannan kuwa ya hada da tun daga kan labara har zuwa fitar fim.

Mun samu fahimta, sannan ra’ayinmu ya zo iri daya a harkar fim. Abinda nake hangowa, shi yake hangowa. Ni da shi muna zama mu yi tunani kan wane irin fim ya kamata mu yi wa al’umma. Wane irin sako mu ke son isawar? Kwanan nan muka kammala daukar shirin Hauwa Kulu, wanda muke sa ran fara tunani shi a sinima ranar Idin Babbar Sallah. Fim ne da muka yi shi a harkar fyade, wadda tana cikin manyan matsalolin suka addabi kasarmu a halin yanzu.

Kana ganin akwai daraktocin da ba su samar maka da abinda kake so shi ya sa ka zabi Ali Nuhu?

Yadda abinda yake shi ne, a iya aikin finafinai da na yi a Kannywood wanda na yi da daraktoci daban-daban, magana ta gaskiya Ali Nuhu na daban ne a cikin daraktoci. Abinda nake nufi shi ne, Ali Nuhu zai tsaya ya tabbatar da ya duba labara tare da gyara inda ake da matsala. Sannan zai saka kansa sosai don ganin an yi amfani da jaruman da suka dace. Idan aka shuti, yana dagewa ya yi aiki tamkar nasa. Duk dai zai fito a matsayin jarumi, hakan bay a hana shi zage jiki wajen bada umarni mai kyau.

Baya ga wannan, zai tsaya a tsara tallan fim din, yana mayar da hankali sosai a wurin tacewa don gudun kuskure. Zirga-zirga ko ina don ya tabbatar da an samu abinda ake so. Hatta wurin tallata fim dinka a kafafen yada labarai, zai dage ya yi iya yinsa, yayin wasu daraktoci da sun gama daukar fim za su bar furodusa da kayansa, babu abinda ya shafe su da sauran harkokin. A wurin Ali Nuhu na daban ne a cikin daraktoci.

Me ya sa kake bawa waka muhimmanci a wasu daga cikin finafinanka?

Yawanci finafinan da muke saka wakoki da yawa, shida, biyar, bakwai, fim ne na soyayya. Wanda mutanen da kake so ka ja hankali su kalla samari ne da ‘yan mata. Saboda haka idan ka yi amfani wakoki masu dadi, za ka janyo hankali su, su kalli fim din, a lokaci guda kuma ka isar da sakon da kake bukata.

Me ya za ke game da nasarar fim din Hauwa Kulu?

Hakika babu abinda za mu yi wa Allah sai godiya. Mun shirya fim din Hauwa Kulu don al’umma, kuma al’ummar ta amsa kira. Babu abinda za mu ce sai godiya. Kamfaninmu na Maishadda Global Resources ba zai yi kasa a gwiwa ba wajen ci gaba da shirya finafinan mai kyau ba.

Ban yi mamakin nasarar da fim dina ya samu ba. Mun shirya kuma mun yi tsari sosai kafin mu kaddamar da shi. A cikin finafinai kusan 10 da na kai Sinima, babu wanda ya samu karbuwar Hauwa Kulu ya samu.

ku duba asalin wannan posting din daga babban shafin mu Ali Nuhu Yafi Daraktoci Da Yawa Iya Bada Umurni – Abubakar Bashir Maishadda mun dauko wannan posting din daga babban shafin mu wato ArewaFresh.com.


©Arewafresh

Post a Comment

 
Top