Likitocin jami’ar Ohio dake kasar Amurka sun bayyana cewa aske gashin gaba bashi da alaka da kamuwa da cututtukan sanyi da ke ta yawan yadawa.

Likitocin sun gano haka ne bayan gudanar da bincike a jikin mata 214 dake aske gashin gaban su kuma suke karatu a jami’ar.

Jagoran binciken Jamie Luster ya ce sakamakon binciken ya nuna cewa kashi 10 bisa 100 daga wadannan mata na dauke da cutar sanyi sannan ga dukkan alamu wannan kason sun kamu da cutar ne a yawan saduwa da maza daban-daban.

Luster yace sun gudanar da wannan bincike ne domin gano ko akwai wani alaka tsakanin yawan aske gaban da kuma kamuwa da cututtuka irin na kamar yadda wasu likitoci suke gargadin mata su daina gaggawar aske gasin gaban su.

Ya ce wadannan likitoci sun bayyana cewa aske gashin gaba na sa a kamuda cutar sanyi a ganinsu wai barin gashin gaba na kare mace daga kamuwa da cututtuka irin na sanyi.

Likita Luster ya ce bayan gudanar da wannan bincike sun gano cewa hakan ba gaskiya ba ne.

Ya ce amfani da kwarorron roba a lokacin da za a yi jima’I, tsaftace jiki, tsaftace dakin bahaya, gujewa yin amfani da bandakin da bashi da tsafta da dai sauran su ne hanyoyin samun kariya daga kamuwa da cututtuka irin haka.




© Sirrinrikemiji

Post a Comment

 
Top