Ana cewa jikin dan adam kamar wata na’ura ce da aka kirkira wadanda kuma yana da lokacin da za su iya tsayawa.
Yana bukatar kula ta musamman don ya ci gaba da gudanar da aiki kamar yadda ake bukata.
Madarar (Soy milk)tana daya daga cikin sananiya kuma da ta yi fice a duniya yau da ake sarrafata.
Tana dauke da sanadarin (protein) mai yawa da kuma sanadarin (fibre).
Ba abin mamaki bane ganin yadda kwararru akan kiwon lafiya suka ba mutane shawara su rika amfani da ita.
Wani abin sha’awa shine, duk da alfanun da take dashi akan kiwon lafiya, mutane da dama basa yin amfani da ita.
Wannan zai iya kasancewa saboda ana sarrafata ne ta hanyar tatsarta da nika ta sannan a dafa waken soya haka dandanonta kamar na madara yake.
Ga wasu daga cikin alfanun da take dasu ga tsofaffin da suka yi ritaya daga aiki:
Lafiyar Zuciya: Tana taimakawa zuciyar jikin dan adam da wasu sassan jikin sa. Sanadarin ta na (Calories) da jimlar kitsen da sanadarin(protein) bai da yawa.
Bugu da kari, tanada kitsen dake taimakawa wajen tura jinin a jikin mutum tana kuma dauke da sanadarin (cholesterol).
Sinadarin Antiodidants: Tana dauke da sanadarin(isoflabones) dake taimakawa sanadaran (antiodidants) mai yawa.
Bincike ya nuna cewar, wannan sanadaran na (antiodidants) suna taimakawa wajen rage sanadarin(odidatibe) dake janyowa mutum jin gajiya da yiwa cell illa da liba sakamakon sanadarin na(odidatibe) mai dake haifarwa da mutum gajiya.
Bugu da kari, a wani dogon bincike da aka gudanar ya nuna cewar za ta iya taimakawa wajen rage alamar (menopausal) ga mata.
Rage Kiba: Tana taimakawa wajen rage kiba da nauyin jiki, musamman ga maza da mata dake da alamomin (postmenopausal).
Tana kuma rage yawan Sikarin dake jikin mutum, idan aka kwatanta da sauran madara da aka fi sani da sanadarin (acids) dake cikin ta da kuma janyo dakatar da fitar kitse wajen rage kiba.
Garkuwa Ga Cutar Kansa: Binciken da aka gudanar ya kuma nuna cewar, shan ta yana taimakawa wajen rage yawan sanadarin (serum estrogen), wanda aka danganta cewar daidai yake wajen janyo Kansa nono.
Mace mai alamar (Post-menopausal) tafi saurin kamuwa da Kansa nono,inda madarar ta (soy milk) zata iya taka muhimmiyar rawa wajen cike makwafin sanadarin (estrogen).
Sanadarin (isoflabones) dake cikin ta yana taimakawa matuka wajen cire ababen da zasu iya zama barazana wajen haifar da Kansa mafitsara ga maza.
© Sirrinrikemiji
Post a Comment