Wani magidanci a jihar Naija da jami'an tsaro suka kama da laifin kashe matarshi me suna, Uwani Danjuma ya amsa laifinshi inda yace ya kashe matar tashi, Uddu ne saboda cemai da tayi daya mutu zata auri wani mijin a lokacin da yayi wata rashin lafiya a baya.

Uwani Danjuma ya kara da cewa, na ji takaicin maganar data gayamin cewa wai idan na mutu zata auri wani mijin. wannan yasa na sassareta da adda a wuya wanda hakan yayi sanadiyyar mutuwarta.

Uwani Danjuma ya kara da cewa be yi nadamar kashe matar tashi ba tunda so take ya mutu, ya kashetane saboda kada ta samu damar yin aure bayan ya mutu, be kamata ta gayamin irin wannan maganar ba dan haka yasa dole ta mutu kuma nasan Allah zai saka ta a wuta saboda abinda ta gayamin, injishi.

Post a Comment

 
Top