Daga Wakilinmu Yaseer Kallah

An daga ranar auren jarumin fim din Hausa, Adam A. Zango, na shida zuwa bayan bikin karamar Sallah.

Jarumin ya wallafa sanarwar daga bikin nashi a shafinsa na Instagram a yammacin ranar Talata.

Zango ya ce: "Assalamu Alaikum 'yan uwa da abokan arziki. Ina sanar da ku cewa an daga aurena har sai bayan Sallah. Za a sanar da ku ranar da aka sake tsayarwa.

"Wadanda ke shirin halartar auren su dakata. Na gode sosai sannan Allah ya shige mana gaba."

Idan ba a manta ba, rahotanni sun bayyana cewa Adam A. Zango ya kammala shirinsa na yin aure a karo na shida. Katin dauren auren ya nuna cewa Zango zai auri wata yarinya mai suna Safiya Umar Chalawa, wadda ake wa lakabin Sufy, da misalin karfe 2:30, ranar Juma'a mai zuwa, a babban Masallacin Sarkin Gwandu, jihar Kebbi.

Sai dai har ya zuwa yanzu ba mu samu takamaimai din dalilin da ya sanya aka daga ranar auren ba.

©HausaLoaded

Post a Comment

 
Top