A abubuwan da muka yi magana a kansu da suka shafi kwalliya, ayaba na daya daga cikin abubuwan da ba muyi magana a kanta ba. Don haka ne a yau na dauko ayaba domin a san irin sinadaran da take dauke da su da kuma yadda za a yi amfani da ita wajen gyaran fata. 

Ayaba na dauke da sinadaran bitamin C kuma tana taimakawa wajen fitar sabuwar fata a lokacin da aka ji rauni.

Ayaba na magance cizon kudin cizo a jiki. Kudin cizo na yi wa fata lahani sosai don haka, sai a samu ayaba a shafa a wajen da aka yi cizon.

Idan an fadi a kan keke fata ta dan kwarzane, sai a samu bawon ayaba a shafa a wajen. Ayaba na taimakawa wajen warkar da wajen ba tare da barin wani tabo ba.

Ayaba na taimakawa wajen sanya hakoranmu haske; bayan an wanke baki da magogi, sai a samu bawon ayaba a goga a kan hakorin. Idan ana yin haka na tsawon mako biyu za a ga cewa hakoran sun kara haske.

Bawon ayaba na warkar da irin kwarzanen da ake samu a wajen soshe- soshen fata.

Masu yawan kurajen fuska da na jiki, sai a samu bawon ayaba ana shafawa a fuska da jiki a kullum kafin a kwanta barci. Washegari sai a wanke. Za a ji sauki a cikin kwanaki kadan.

Ko an san cewa bawon ayaba na magance ciwon kai? A samu bawon sannan a dora a inda kan ke harbawa na tsawon minti 30 za a ji sauki.

Bawon ayaba na magance kaikayin fata. A shafa bawon a kan kurajen.

Ayaba na taimakawa wajen haskaka takalmanmu. Ko za a gwada ne sannan a ba ni labari. Bayan an goge takalmi da tsumma sai a dauko bawon ayaba a goga a jikin takalman za a ga takalmin ya fara sheki.



© Sirrinrikemiji

Post a Comment

 
Top