Shugaban kungiyar ta’addanci na Boko Haram, Abubakar Shekau ya yi barazanar kashe babban malamin Ahlussunnah, kuma ministan sadarwa, Isa Ali Pantami da fitaccen mai fashin baki a kan kungiyar Boko Haram, Audu Bulama Bukarti.

 Shekau ya bayyana haka ne cikin wani sabon bidiyo daya fitar mai tsawon mintuna 15 da dakika 20, inda ya yi amfani da damarsa ya caccaki Sheikh Isa AliPantami, kamar yadda jaridar Daily Nigerian ta ruwaito.

Shekau ya kalubalanci Pantami kan cewa ba shi da hurumin yin magana da yawun Musulunci, sa’annan ya bayyana shi a matsayin mutumin dake ma kafirai aiki, haka zalika ya soki lamirin Pantami na kirkiro dokar hana mallakar layukan waya da suka wuce uku.

 Shekau ya tuna ma Pantami yadda suka kashe Sheikh Jaafar Adam, wanda aka bindigeshi a yayin da yake sallar Asubah a Masallacinsa dake Kano, sa’annan ya yi kira ga sauran yan ta’adda dake Afirka dasu shiga farautar Pantami a duk inda suka gan shi.

 “Ya yan uwana dake nahiyar Afirka, Najeriya da ma ko ina, abinda muka ma Jaafar ba wani abu bane, dole ne a yanzu mu dauki mataki a kan Pantami a duk inda muka gan shi.” Inji shi.

Bugu da kari Shekau ya gargadi shugaban kasa Muhammadu Buhari, babban hafsan sojan kasa, Laftanar Janar Tukur Yusuf Buratai, gidan rediyon BBC, rediyon DW, rediyon Faransa da Dandan Kura Radio.

Ya cigaba da cewa: “Bulama Bukarti da kake Ingila, na san ka samu sakona, kai din karamin kwaro ne, ko iyayen gidanka ba zasu iya fada damu ba.” Ko a ranar 1 ga watan Nuwamba ma sai da Shekau ya yi barazanar kashe Bulama, inda yace: “Ka shiga uku, ba zaka sake samun zaman lafiya ba.”

Shekau da Boko Haram sun sanya ma Bulama idanu ne sakamakon tarin ilimin da yake da shi game da kungiyar Boko Haram da sauran kungiyoyin ta’addanci, yana yawan tattaunawa a hirarrakin gidajen rediyo tare da wallafa rubuce rubuce a kan Boko Haram.

©HausaLoaded

Post a Comment

 
Top